Umar A Hunkuyi" />

Kotu Ta Warware Auren Shekara 41 A Kan Aikata Alfasha

A ranar Alhamis ce, Wata kotun al’ada da ke Legas, ta warware wani Auren da ya shekara 41 a tsakanin wani Limamin Kirista, Pasto Richard, da tsohuwar matarsa mai suna, Mabel Alli, a bisa zargin aikata alfasha. Alkalin kotun, Mista Adeniyi Koledoye, cewa ya yi, tun da dai a bisa ga dukkanin alamu ma’auratan sun gaji da zama da junansu ne duk kuma wasu hanyoyi na a daidaita su da aka bi sun ci tura.
“Tun da dukkanin su biyun sun amince da a raba auren, kotu ba ta da wani zabi face ta bata wannan auren. “Don haka, kotu tana shelanta zaman aure a tsakanin Mabel Alli da Pastor Richard, a matsayin batacce. Daga yau, babu sauran aure a tsakanin ku.
“Kowannen ku sai ya kama gabansa. Kotu kuma tana yi ma kowannen ku fatan alheri a kan duk inda ya sa gaba,” in ji Alkalin kotun. Ita dai matar da ta shigar da karan neman kotun ta warware auren na su mai suna Mabel Alli, ta shaidawa kotun ne cewa, mijin nata mai suna Richard, ya yi wa kanwarta da kuma diyar da suka Haifa a tare, ciki. “Mijin nawa, ya yaudari tare da cin zarafin ‘ya’yan da muka haifa tare da shi, mata su uku, inda ya yi zina da su. Bayan da ya yi wa kanwata ciki, sai ya dauki daya daga cikin ‘yan’yanmu mata zuwa Asibiti, domin a zubar mata da cikin da ya yi mata. “Ita ma daya diyar tamu mai shekaru 19, ta labarta mani yanda yake sadadawa dakinta a kowane lokaci yana yin lalata da ita, har ta kai ga na kama shi da ido na turmi-da-tabarya da ita.
“Kawaye na da masu yi mana hidima a cikin gida duk bai barsu ba. Ba wacce ban kama shi yana lalata da su ba, shi cikakken manemin mata ne. ‘Yar kasuwar mai shekaru 63, ta ce, Mijin nata kuma matsafi ne, ya ma so ya yi amfani da ita wajen neman kudi ta hanyar tsafi, domin ya sami kudin da zai yi kamfen din siyasar sa da su.
Mabel ta yi zargin cewa, Mijin nata kuma sam ba ya nuna damuwarsa a kan ‘ya’yan na su. Matar mai ‘ya’ya hudu, sai ta roki kotun da ta warware Auren na su inda take cewa, ba ta kuma kaunar zama da mijin nata.
Sai dai kuma, Mijin nata mai suna Richard, wanda ya musanta duk zarge-zargen da matar na shi ta yi ma shi, ya yi maraba da batun bata Auren na su, inda shi ma ya ce, bay a kaunar ci gaban zaman auren na su. Paston mai shekaru 66, ya musanta batun yana yin lalata da kanwar matar na shi, kawayenta, masu yi masu hidima a cikin gida, ballantana ‘ya’yan da suka Haifa, yana mai cewa, matar na shi ce dai ta kai diyar tasu zuwa wajen zubar da cikin. A cewar shi, bai taba kai matar na shi zuwa wajen wani boka ba, bai kuma taba yin barazanar kashe ta ba. A maimakon haka, ya ce ya dai yi tafiya ne zuwa kasar Kenya domin halartar wani taron addu’a, amma ba wai ya je ne domin nemo wani tuggun da zai kashe matar na shi da shi ba, kamar yanda take zargi.

Exit mobile version