Daga Rabiu Ali Indabawa,
A ranar Talata yankewa wani matashi mai shekaru 21 mai suna Timiondu Jephtath hukuncin daurin shekaru 10 a wata babbar kotun Jihar Bayelsa da ke zaune a Sagbama, Yenagoa saboda yi wa yarinya ‘yar shekara biyar fyade har ta lahira.
Majiyarmu ta samu labarin cewa matashin mai shekaru 21 ya yi wa yarinyar fyade har sai da ta mutu a garin Akede da ke karamar hukumar Sagbama ta jihar a shekarar 2016.
A cewar rahoton, wanda ake zargin mai suna Jefta wanda ya kasance a lokacin yana da shekara 16, ya jefa gawarta a cikin wani kududdufi da ke kusa da gidansa bayan ta mutu.
Lauya kuma mai bin jinin wacce aka kashe din, Deme Pamosoo, wanda ya yi aiki a matsayin mai ba da shawara ga iyayen wanda aka kashe din ya tabbatar da cewa an gano gawar wacce aka azabtar din, a binciken da ‘Yan Sanda suka gudanar da kuma shigar da karar, wadda tuni aka gabatar wa Daraktan Ma’aikatar Shari’a ta Jiha.
Alkalin da ke jagorantar shar’ar, Mai Shari’a EG Omukoro a hukuncin da ya yanke a karar mai lamba SHC/4C/2016 tare da tuhuma guda daya na kisan kai da Ma’aikatar Shari’a ta Jihar ta gabatar, ya bayyana cewa tuhumar ta zama kisan kai saboda ba kisa ne da aka yi shi da niyya ba.
A hukuncin da ya yanke, bayan la’akari da rokon da wanda ake kara ya yi, mai shari’a Omukoro ya bayyana cewa kotun na tuno da shekarun samartaka na wanda ake kara wanda za a iya fansa da shi kuma a yi gyara ta hanyar kaffarar abin da ya aikata.
Don haka, ya bayar da umarnin a tsare wanda ake tuhuma a Cibiyar Gyara hali ta Okaka a Yenagoa ko kuma wani wuri na daban.
Da take maida martani kan hukuncin, mukaddashin shugaban kungiyar mata ta kasa (FIDA), Misis Ebimietei Ekeowei Ottah, ta bayyana hukuncin a matsayin nasara ga wadanda aka yi wa fyade, da cewa kazanta ne da cin zarafin mata a jihar.
“Babban gargadi ne ga sauran jama’a cewa yanzu aikata hakan ba zai zama kasuwanci kamar yadda aka saba a jihar Bayelsa. Da zarar an gurfanar da kai a gaban doka, doka za ta dauki matakinta kuma ta kumaa tsare ka, ”in ji ta.
“Ya kasance aiki ne mai matukar wahala a jihar Bayelsa kuma abin da ya fi damuwa shi ne batun tattaunawa tare da masu laifi daga iyayen wadanda aka lalata ko kuma yi wa ‘ya’yansu fyade. Ba za a iya sake jure shi ko sharewa ta karkashin shimfidar sulhu ba. Muna kira ga iyaye, malamai, makwabta da masu kula gami da sa ido sosai sannan su yi magana game da batun fyade, cewa kazanta ne da cin zarafin mata a cikin jihar. ” a cewarsa.