Bello Hamza" />

Kotu Ta Yanke Wa Wani Matashi Hukuncin Bulala 12 Saboda Satar Doya

doya

Wata kotun yanki da ke Zuba, Abuja, ta yanke wa wani matashi mai suna Hashirmu Babagida, hukuncin bulala 12 saboda satar doya da aka kiyasata kudinta ya kai Naira 596,000.

‘Yan sanda suna tuhumar Babangida ne, wanda yake zaune a unguwar Dankogi Garage, Zuba, da laifin sata.

Da yake yanke hukuncin, alkalin kotun Malam Gambo Garba ya gargadi Babangida akan ya sauya halinsa ya zama mutumin kirki ya daina sata.

Tun da farko, lauya mai gabata da kara, Mr Chinedu Ogada ya bayyana wa kotun cewa, a ranar 27 ga watan Disamba 2020, wani mai suna Tanko John, ya kai rahoton satar da aka tafka masa a ofishin ‘yan sanda dake Zuba.

Ogada, ya kuma kara bayyanawa kotun cewa, a ranar 26 ga watan Disamba ne Babangida ya tsallaka gonar doyar John da ke Zuba Abuja, inda ya saci doyar da aka kiyasata kudinta ya kai Naira 596,000.

Ya kuma ce, binciken da aka gudanar ya nuna cewa. Babangida ya aikata laifin ya kuma amince da aikata laifin da kansa, an kuma samu nasara kwato doyar da ya sata a gidansa.

Mai gabatar da karar ya kuma ce, laifin ya saba wa shashi na 287 na dokar Fanel Kot.

 

Exit mobile version