Kotu Ta Yi Fatali Da Kararrakin Tube Magu Daga EFCC

A ranar Laraba ce, babban kotun tarayya da ke garin Abuja ta yi fatali da bukatar neman a cire Mista Ibrahim Magu a kan mukaminsa na mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC). A wannan kara na neman tube Magu daga mukaminsa, sau biyu majalisa tana kin amincewa da mukaminsa, ta yadda zai gudanar da aiki yadda ya kamata. Shi dai Magu yana matsayin makaddashin hukumar EFCC tun shekarar 2015, tun da sajalisa ta ki amincewa da shi.

Da take gabatar da shari’ar, alkali mai shari’a Ijeoma Ojukwu, ta bayyana cewa, akawai dokar da ta ba shi dama ya ci gaba da rike mukaddashin shugaban hukumar EFCC. Ta bayyana cewa, ko da yake dokar ba ta amince Magu ya gudanar da ayyuka yadda ya kamata ba, ba tare da majalisa ta tantance shi ba, tun da shugaban kasa ya nada shi, yana da wuka da nama da zai gudanar da aiki a matsayin shugaban EFCC.

Exit mobile version