Jam’iyya mai mulki a Kenya, ta nemi wata kotu ta yanke hukuncin kin bin umurninta akan madugun ‘yan adawar ƙasar Raila Odinga, inda ta yi iƙrarin cewa Odinga da magoya bayansa, suna zagon-ƙasa ga zaɓen shugaban ƙasar da za a sake a makon da ke tafe.
Jam’iyyar ta Jubilee ta shigar da ƙarar ne a gaban kotun ƙolin ƙasar a jiya, yayin da Odinga ya tsaya tsayin-daka akan cewa shi da gamayyar jam’iyyu ta NASA ba za su shiga zaɓen ba wanda za a yi a ranar 26 ga watan Oktoban nan.
A cewar Odinga, hukumar zaɓen ta IEBC, ba ta shiryawa zaɓen ba, saboda haka, “a maimakon a yi wannan kwamacalar a barnatar da kuɗaɗen jama’a da lokaci, ya fi mana mu janye daga zaɓen,” kamar yadda shi Odinga ya faɗawa manema labarai.
Sai dai kuma a jiyane, Sakatare-Janar na jam’iyyar Jubilee da ke mulki, Rapahel Tuju, ya ce har yanzu Odinga bai miƙa wa hukumar zaɓen wasiƙar janyewa ba.