Kotun koli ta tabbatar da zaben Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule.
Idan ba a manta ba a baya kotun sauraron kararrakin zabe a jihar ta kori gwamnan tare da bayyana abokin hamayyarsa, David Ombugadu, na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar 18 ga Maris, 2023.
- Kotun Ƙoli Ta Sake Tabbatar Da Zaɓen Abiodun A Matsayin Gwamnan Ogun
- Kotun Koli: PDP Da APC Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Nasarawa
Daga bisanu Kotun daukaka kara ta mayar da Gwamna Sule nasarar zabensa da karamar kotun ta yi na kuskure a hujjoji takwas daga cikin shaidun PDP.
Talla
Kazalika, a yau Juma’a, kotun kolin bisa jagorancin mai shari’a, Kudirat Kekere-Ekun, ta ce karar da dan takarar PDP ya shigar ba ta kan tsari.
Talla