Kotun Da’ar Ma’aikata CCT Za Ta Saurari Kararraki A Bauchi

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Kotun da’ar ma’aikatan Nijeriya wato CCT za ta gudanar da zamanta domin sauraron kararrakin da suke gabanta kan ma’aikata da kuma masu rike da mukaman siyasa da suka gaza bayyana kaddarorinsu na hakika a jihar Bauchi.

Zaman da korun za ta yi a jihar Bauchi zai gudana ne a tsakanin ranakun 24 zuwa 27 na watan Afrilun da muke ciki.

Hakan yana kunshe ne a cikin wata sanarwa daga kotun da’ar ma’aikatan, wacce Ahmad Abdullahi ya sanya wa hanu a madadin jami’in da ke kula da harkokin kotun ta CCT a jihar Bauchi, sanarwar wacce aka raba wa ‘yan jarida a Bauchi.

Sanarwar ta kuma ce shugaban kotun CCT, Mai Shari’a Danladi Umar shine zai jagoranci zaman na kotun domin sauraron shari’un hade da yin aikinsu yadda kotun take tafiya a kai.

Kotun dai za ta saurari kararraki akan masu rike da mukaman siyasa hade da ma’aikatan gwamnati wadanda suka gaza bayyana kaddarorinsu wa hukumar kula da da’ar ma’aikata hade da wadanda suka buye gaskiyar kaddarorin da suka mallaka na hakika a hukumar.

Kotun dai za ta gayyaci dukkanin wadanda abun ya shafa domin kare kai daga kararsu da aka yi.

Exit mobile version