Umar A Hunkuyi" />

Kotun Da’ar Ma’aikata Ta Bada Umurnin Kamo Onnoghen

Kotun da’ar ma’aikata ta bayar da umurnin kamo tsohon Alkalin Alkalai na kasar nan wanda aka dakatar, Walter Onnoghen.
A sa’ilin da Kotun ta dawo zamanta ne a ranar Laraba, ta bukaci hukumomin tsaro na kasar nan da su hanzarta kamo Walter Onnoghen, a dalilin kin halartan kotun da ya yi.
Lauyan gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin, Aliyu Umar, sun nemi kotun ne da ta bayar da umurnin kamo, Walter Onnoghen, a bisa gazawar da ya yi na zuwa kotun.
Wannan shi ne karo na biyar da dakataccen Mai Shari’an ya gaza zuwa kotun tun daga lokacin da aka fara shari’ar.
Gwamnatin tarayya tana tuhumar sa ne da karya wajen bayyana kadarorin sa.
Da yake bayyanawa kotun bukatar na su na a bayar da umurnin kamo Onnoghen din, Umar ya koka ne a kan yanda Onnoghen din yake ci gaba da kin halartar kotun.
Ya ce, daga tsarin tafiyar da shari’ar wanda ya aikata laifi har zuwa ga tsarin ita kanta wannan kotun ta da’ar ma’aikata, duk sun bukaci kasantuwar wanda ake wa shari’a a cikin kotu kafin ci gaba da yi ma shi shari’a a kan abin da ake tuhuman sa da shi.
Lauyan da ke jagorantar Lauyoyin da suke kare wanda ake kara, Adegboyega Awomolo, ya nemi kotun da ta yi watsi da bukatar hakan.
Onnoghen ya nemi Umar da ya sauka daga shugabancin shari’ar a kan dalilin, “akwai yiwuwar yin son kai daga gare shi.”
Amma, sai Umar ya ce ma shi, shi da sauran wakilan kotun ba ma’aikatan shari’a ne ba, don haka, hukumar shari’a ta kasa ba za ta iya ladabtar da su ba.

Exit mobile version