Kotun Da’ar Ma’aikata Ta Samu Tsohon Alkalin Alkalan Nijeriya Da Laifi

Kotun Da’ar Ma’aikatan Nijeriya ta samu tsohon babban jojin Nijeriya da laifin kin bayyana kadarorin shi yayin karbar aiki, kamar yadda dokar kasa ta tanada.

Alkalin kotun mai Shari’a Danladi Umar ya bada odar sauke Walter Onnoghen daga mukamin shi na alkalin alkalan Nijeriya ba tare da wani bata lokaci ba.

Sannan kotun ta bada umarnin a cire shi daga dukkan mukaman shi, mukaman da yake rike da su a baya sun hada da shugaban kungiyar alkalai ta kasa, da kuma shugabancin hukumar alkalai ta Nijeriya.

A biyo mu don samun cikakkun labarai…

Exit mobile version