Connect with us

LABARAI

Kotun ECOWAS Za Ta Fara Zama Don Yanke Hukunci Ta Intanet

Published

on

Bayan dakatar da zama na wata uku don kaucewa yaduwar annobar cutar korona, Babbar Koton kasashen Afrika ta Yamma ECOWAS ta ayyana fara zama don yanke hukunci a ranar Litinin 22 ga watan Yuni 2020. Sanarwar da ta fito daga sashen yada labarai na kotun ranar juma’a ta bayyana cewa, a zaman da za a fara ranar Litinin ana sa ran yanke hukunci a kan shari’a 10 dake gabanta.
Tuni shugaban kotun, Hon. Justice Edward Asante, ya bayar da umarcin fara gwajin kaya aikin inatet din, ta yadda za a gudanar da zaman kotun ba tare da wata mastala ba.
Shugaban kotun Justice Asante, ya kuma bayyana cewa, ya zama dole kotun ta yi amfani da kimiyyar sadarwa wajen gudanar da ayyukan ta musammaman a inda haduwa yake da wahala sakamakon barazanar yaduwar cutar korona.
Ya ce, an kuma yi haka ne don a kara dakile yadda cutar ke yaduwa, musamman ganin ana son tabbatar da adalci a cikin al’umma.
“Dokokin da ta kafa kotun sun halasta amfani da kafar sadarawa na zaman wajen gudanar da ayyukan kotun, muna kuma sa ran yanke hukunci a kan shari’a da dama a ranar da za a kaddamar da gufana da shari’a wato ranar Litinin,” inji shi.
Shugaban kotun ya kuma ce tuni aka samar da kayyakin aiki da ake bukata tare da kuma horar da ma’aikata da kuma lauyoyin kasashen kungiyar wadanda suka shigar da kara a gaban kotun.
Ya kuma kara da cewa, an gudanar da zaman kotun na gwaji don ganin yada kayan aikin suke don kaucewa fadawa matsala.
Asante ya kuma lura da cewa, fara aiki da fasahar intanet wajen ayyukan kotun zai taimaka wa ‘yan kasashen yankin na Afrika wajen shigar da kara ba tare da sun zo har harabar kotun, musamman ganin irin tsadar da hakan yake iya haifarwa ga al’umma.
“Muna da tabbabacin fara aiki da fasahar zai yi matukar taikamawa, da sukaka ayyukan kotun.
“Zai rage kudaden da ake kashewa wajen shigarwa da kuma gabatar da kara wanda hakan yana dakile muradin masu neman adalci a kan zalunci ko hakkin da suke nema,” inji shi.
A zaman kotun na ranar litnin za a yanke hukunci akan shari’a 10 wanda aka shirya yanke hukunci su a watan Maris tun da farko amma aka dakatar soboda batun cutar korona.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: