Sagir Abubakar" />

Kotun Katsina Ta Dage Shari’ar Mahadi Shehu Da Mustapha Inuwa

Mahadi Shehu

Babbar Kotun Jihar Katsina ta dage sauraren shari’ar dake tsakanin Mahadi Shehu da Mustapha Muhammad Inuwa zuwa ranar 25 ga Janairu, 2021.

Wakilin LEADERSHIP A YAU ya ruwaito cewa kotun da ke da alkalai uku a karkashin Mai Shari’a Hajaratu Hajjo Lawal ta bayyana dage sauraren shari’ar a zaman da suka yi a jiya.

Kamar yadda rahoton yace, dage sauraren karar ya biyo bayan wata bukata da lauyan Mahadi Shehu ya yi Barrister Abbas Abdullahi Machika da yake neman kotu da ta janye wata takar koke da aka gabatar a gabanata.

Abbas Machika ya shaidama kotun cewa samun wata takarda ba daga waccan kotun da ta bada umarnin a kama wanda ya daukaka karar.

Lauyan ya kuma roki kotun da ta kori batun da aka fara kawo mata sannan kuma ya roki wasu batutuwan guda.

Jimkadan bayan gama zaman, duka lauyoyin (2) na bangaren wanda ya daukaka karar Barista Abbas Machika dad a kuma na dayan bangaren Ibrahim Shehu sun amince zasu bi alkalin zuwa Funtua don cigaba da sauraren shari’ar ranar (25) ga wannan wata na Janairu da muke cikin.

Idan za’a iya tunawa dai Mahadi Shehu ya daukaka kara yana kalubalantar hukuncin da kotun shari’a ta yanke wanda ta bada umarnin a kamoshi sakamakon rashin bayyana a gaban kotun lokacin zaman sauraren kara da tayi a wasu makwanni da suka gabata cikin shekarar da ta gabata.

Kotun ta bada umarnin a kamo Mahadi Shehu a kawo shi gabanta taa karfi sakamakon kararshi da Mustapha Muhammad Inuwa ya kai akan yana cin zarafim sshi kuma yana bata mashi suna a shafukan sada zumunta na zamani.

Exit mobile version