Connect with us

MANYAN LABARAI

Kotun Kolin Kasar Indiya Ta Halasta Zina

Published

on

Kotun kolin kasar Indiya ta yanke hukunci akan zina, inda ta bayyana ta a matsayin ba laifi ba da in mutum ya aikata, zai fuskanci hukunci, amma dai in mai aure ya aikata zinar to dole zai rabu da matarshi, ko mata zata rabu da mijinta.

A wata doka mai shekaru 158, duk mai auren da ya aikata zina to zai fuskanci hukunci dauri a gidan yari na tsawon shekaru biyar, duk da a wasu kasashen masu makwabtaka da Indiya zina har yanzu laifi ce, misali kasar Taiwan, da kasar Pakistan da ma Bangladesh.

Dadin dadawa Kotun ta sake fasalin dokokin da suka shafi ma’aurata, inda yanzu mata zata iya kai karar mijinta in ya yi mata abinda ya saba da zaman auren su, wanda a da babu wannan tanadin a cikin dokar kasar.




Advertisement

labarai

%d bloggers like this: