Khalid Idris Doya" />

Kotun Sauraron Kararrakin Zabe Ta Tabbatar Da Kaura A Matsayin Gwamnan Bauchi

Gwamnan Bauchi
Kaura yayin da yake sujadar godiya ga Allah bayan Hukuncin kotun

Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Bauchi ta tabbatar da Sanata Bala Muhammad Abdulkadir a matsayin gwamnan Bauchi, ta kuma ce, zaben da aka yi na gwamna a 2019 sahihin zabe ne mai cike da gaskiya.

A hukuncin da kotun ta yanke na tsawon awa shida (7), ta ce, karar da tsohon Gwamnan Bauchi, Muhammad A. Abubakar ya yi akan gwamna mai ci, Sanata Bala Muhammad kara ne wanda bai da inganci.

kotun mai Alkalai uku da ke karkashin shugabancin Justice Salihu Shuaibu ta kori karar da cewa masu kara sun gaza tabbatar da abun da suke zargi na magudin zabe. Kotun ta ce zargin da M.A ke yi bai tabbatar ba, kuma bai inganta ba domin gaza tabbatar da shaidu kan ikirarin na masu kara.

Kotun dai ta kori mafiya yawa daga cikin shaidun da APC ta gabatar, gabanin ta yanke hukunci nata.

Wakilan kowani bangare sun kasance a kotun a lokacin da Alkalin ke yanke hukuncin nasa.

Tun da safiyar yau da karfe 10 har zuwa karfe 4.50pm na yammaci Litinin kotun ta ke jawabin yanke hukuncin da ke tsakanin Barista M.A na APC da Sanata Bala na PDP.

Kotun ta tabbatar da dan takarar jam’iyyar PDP Sanata Bala Muhammad a matsayin gwamnan jihar Bauchi.

Lauyoyin kowani bangare suna ganawa da ‘yan jarida, sai dai Lauyoyin PDP sun yaba wa kotun a bisa wannan hukuncin da ta yanke.

Cikakken labarin na biye.

Exit mobile version