Daga Umar Faruƙ, Birnin Kebbi
Matasa goma sha ɗaya ne wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Kebbi cikin Jihar Kebbi ta sa aka kulle a bisa zargin hana zaman lafiya a garin Zauro.
‘Yan sanda ne suka kama matasan lokacin wani taro da dattawan na gari Zauro suka gudanar a Fadar Dagacin yankin don magance yawaita laifufukan fyaɗe da sace-sace da shan kayan maye da sauran laifufuka tsakanin matasan yankin.
Ɗaya daga cikin shaidun, Insifeto Ishaka Abdullahi wanda shine ke shugabantar ofishin ‘yan sanda na garin Zauro, ya shaidawa kotun cewar, lokacin da dattawan ke kan gudanar da taron, matasan sunyi ƙoƙarin kutsawa inda ake gudanar da taron, amma ‘yan sanda wurin suka taka masu birki, inda matasan suka dinga yin jifa kan mai uwa da wabi da Duwatsu da fasassun kwalabe da dukkan abin da suka wawura a wurin, har ta kai ga sun lalata motar ‘yansanda.
Mai Samari wanda ya cigaba da cewa matasan sun kuma yi barazanar cewa ba za su yi biyayya ga dukkan wata doka da dattawan za su kafa ba, a bisa iƙirarinsu na cewar dokar zata tsaya ce kawai, akan ‘ya ‘yan talakawan yankin ta kuma ƙyale ‘ya ‘yan masu hannu da shuni da ke wannan yankin.
A cewar Ɗan sanda mai ƙorafi, Faruk Muhammad wanda ke wakiltar rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, ya ce matasan ana zargin su da kulla munafunci da kawo hatsaniya a gari, wanda ya kamata a hukunta su a bisa doka ta sashe 97,113 da kuma doka 149 ta ‘’penal code’’
A nashi ɓangaren, lauyan matasan da ake zargi, Barista Ahmad Zumaru ya bayyanawa manema labarai cewa dattawan ba subi ƙa’ida ba, wajen kafa dokar ta su, domin ba su bi ta hannun ƙaramar hukuma ba.
Ya kuma ƙalubalanci ‘yan sandan akan cewa ba su yi dai-dai ba wajen haɗa kai da al’ummar yankin da suka yi.
Alƙalin Kotun, mai shari’a Mu’awiya Shehu ya ɗaga sauraron ƙarar zuwa ranar litinin mai zuwa domn cigaba da sauraran ƙarar, inda kuma ya umarci da akai matasan 11 ajiya a gidan Yari.