Khalid Idris Doya" />

Kotun Turai Ta Nemi Poland Ta Rage Wa’adin Ritaya Ga Alkalai

Kotun Tarayyar Turai ta bukaci kasar Poland ta janye dokar rage yawan shekarun da Alkalai za su yi ritaya a aiki daga kotun kolin kasar, domin kawo karshen sauye-sauyen da ta aiwatar masu cike da rudani.

Tun shekara ta 2015 aka shiga takun-saka tsakanin Poland da Tarayyar Turai bisa wasu sauye-sauye abin da ya janyo zuwa kotun domin warware sabanin. Tun farko Poland ta rage yawan shekaru da manyan Alkalai za su yi ritaya daga 70 zuwa 65 lamarin da ya haifar da cece-kuce bisa neman ganin wasu Alkalai 22 sun ajiye aiki.

Exit mobile version