Babbar Mai Shari’a ta jihar Bauchi, Alkali Rabi Talatu Umar, ta shaidar da cewar, a karon farko tun kirkirar jihar a shekara ta 1076, kotunan Magistare da na yankuna, yanzu haka ba su gudanar da ayyukan su na yau-da-kullum a muhallai na haya.
Ta ce wadannan kotuna a yau su na da muhallai da ofisoshi nasu a harabar babbar kotu ta jihar, sashi na biyu, wanda samuwar hakan aka danganta shi da kyakkyawan jagoranci na Gwamna Bala Muhammad, tana mai cewar, gwamnan yana taka rawar gani matuka gaya tun lokacin da ya kama ragamar mulki a watan Mayu na shekara ta 2019.
“Bisa kokari da jajircewa ta mai girma gwamna, an kammala ginin sashi na biyu na babban kotun jihar, tare da kawata shi da kayayyakin aiki da suka dace, ginin wanda yake dauke da manyan kotuna guda takwas, ofisoshin manyan Alkalai guda takwas, dakunan ajiye masu laifi da sauran makamantan kayayyaki.”
Babbar mai shari’ar wacce take yin jawabi a wani buki na bude sabuwar shekara ta 2020/2021 a garin Bauchi, shelkwatar jihar a satin da ya gabata, ta ce kotunan majistare guda takwas yanzu hakan sun samu mahallai a unguwar Fadamar Mada, hadi da gyaran manyan kotuna guda biyu da aka gudanar, tare da baiwa dukkan manyan Alkalan manyan kotuna da Khaduna sabbin motocin hawa.
Mai Shari’a Rabi Umar ta kara da cewar, an kuma samar da sabbin motoci guda uku wa sabbin manyan Alkalai da za a dauke su aiki nan bada jimawa ba.
“Manyan Alkalan mu a halin yanzu suna da dakunan gudanar da shari’o’i da kuma sauran kayayyakin aiki da za su saukaka ayyukan na gudanar da shari’a. Mukaddasan Rajistarori, Rajistarori, Daraktoci, Mukaddasan Daraktoci, da sauran manyan jami’ai a halin yanzu su na da ofisoshi nasu, wadanda aka daje su da kayayyakin aiki”.
Justice Rabi ta kuma nusar da cewar, a halin yanzu ana ta shirye-shiryen daukar manyan Alkalai guda biyu da Khaduna guda hudu, wanda ya biyo bayan bukatar yin hakan, tare da sanya hannun amincewar babban mai shari’a na kasa, Justice Ibrahim Tanko Muhammad, domin cike gurbin rashin su.
“Cike wadannan gurabai, zai kuma kara hazakar Alkalan wajen wanzar da shari’a. Muna kuma kokari ala-kulli-yaumin domin inganta tsarin ayyuka tsakanin manya da kananan ma’aikatan shari’a”.
Babbar mai shari’ar ta kuma yabawa da godewa hukumar daukar jami’an shari’a ta jiha (JSC) bisa goyon baya, hadin kai, da aniyar ta na kyautata ayyuka, hadi da tafiyar da lamuran ma’aikata bisa ka’idojin aiki.
Ta kuma bayyana cewar, a shekarar da ta shude, babbar kotu ta jihar ta amshi laifuka manya da kanana guda 341, wadanda daga ciki aka zabe da guda 268, sannan guda 73 na kan tsaiko, kazalika an yi rajistar batutuwa guda 374 wadanda daga ciki aka zazzage 243, kana guda 131 suna kan tsaiko.
Mai Shari’a Rabi Tlatu Umar ta kuma bayyana cewar, kotunan majistare dana yankuna a shekarar da ta gabata sun yi rajistar batutuwa guda 1, 367, wadanda daga ciki suka zazzabe guda 903, kana guda 464 suna kan tsaiko.
Ta kuma bayyana gidan gyara halinka a matsayin wani shingen karshe wa duk wani maluki da ya shiga komar tsaro, walau wanda aka yake wa hukunci ko mai jiran hakan, tana mai cewar gidan gyara halin, yana gudanar da ayyukan sa ne na gyara halayen jama’a da tsuwuiwirar su domin zama mutane nagari a cikin al’umma.