Connect with us

WASANNI

Koulibaly Na Son Koma Wa Liverpool Daga Napoli

Published

on

Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Napoli da ke kasar Italiya, kuma dan wasan tawagar kasar Senegal, ya bayyana burinsa na buga wasa a zakarun gasar firimiya na bana, Liverpool, wadda ta lashe gasar firimiya a ranar Alhamis din data gabata.

A satin daya gabata ne daman Liverpool ta mika bukatar sayen mai tsaron bayan  dan wasan da ke matsayin mai tsaron baya da kungiyoyin Turai ke rububi a yanzu saboda kwarewarsa da kuma yadda ya iya saita ‘yan wasan baya.

Baya ga Liverpool din kungiyoyin Firimiya ciki har da Chelsea da Manchester United na sahun gaba-gaba da suka nuna sha’awar sayen dan Senegal din mai shekaru 29 a duniya, ko da dai Liverpool din ce ta fara tuntubar dan wasan a hukumance.

Idan har Liverpool ta yi nasarar sayan dan wasan  zata hada zaratan masu tsaron baya da ake kallonsu a matsayin mafiya karfi da rashin tsoro wato Kalidou da birgil ban Dijk bayan kungiyar ta  lashe kofin firimiya karo na farko cikin shekaru 30.

“Ina son buga wasa a Liverpool saboda babbar kungiya ce a duniya kuma tun ina matashin dan wasa nake jin labarin kungiyar da abinda ta buga a shekarun baya saboda haka yanzu lokaci yayi d azan koma kungiyar idan har na samu dama” in ji Koulibaly

Koulibaly wanda Napoli ta sanyawa farashin yuro miliyan 90 masu sharhi kan al’amuran wasanni na ganin abu ne mai wuya Liverpool ta iya sayen dan wasan a wannan farashi musamman ganin yadda cutar Korona ta kassara bangaren kudaden shigar kungiyoyin.

Shugaban gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Napoli, Mario De Laurantis, ya bayyana cewa zasu iya sayar da dan wasan bayan nasu amma sai an samu kungiyar da zata iya biyan abinda suke bukata.

Itama kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German ta bayyana bukatarta ta sayan dan wasan bayan da itama kungiyar ta kasar Faransa ta bayyana cewa dan wasanta na baya kuma kaftin, Thiago Silva, zai bar kungiyar a karshen wannan kakar.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: