Daga Muhammad Maitela
Daya daga cikin guguwa mafi karfi a Nijeriya wadda ta fasa lemar jam’iyyar PDP, a lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ita ce zargin kalmshe wasu makudan kudaden da aka ware domin sayo makaman da za a yaki da matsalar tsaron Boko Haram da su ta hanyar wasu jiga-jigan gwamnatin sa, kurar da har yau ba ta lafa ba.
Zargin handame kudaden ya jawo hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Nijeriya (EFCC) ta rinka wasan kura da jami’an tsohuwar gwamnatin PDP, yayin da aka rinka wasan buya da wasu jan-wuya a baya, wanda duk da wannan yar zilliyar amma bai hana hukumar zarge wuyan su zuwa gaban kuliya ba tare da aika daruruwa gidan maza. Kudin makaman a wancan lokacin sun doshi Dalar Amurika Biliyan 2 da yan kai, wanda mutum na gaba-gaba a zargin shi ne tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Kanal Sambo Dasuki.
Bisa ga yawan masu hannu a wannan tsohuwar badakalar handame kudin makaman, aka yi wa sabgar ‘Dasukigate’ kofar da ko a leke mutum ya yi gigin shigarta, to sai dan-buzun shi. Wanda uban gayya a zargin ya sha zaman jarun kamar huhun goro, wanda sai a bayan nan ne kotu ta bayar da belin shi.
Bugu da kari, wannan badakalar makamai ba bisa ka’ida ba ta samu tazgaro ne a binciken da kwamitin shugaban kasa ya bankado dangane da kudin da gwamnatin Jonathan ta ware don sayo makaman. Yayin da rahoton kwamitin ya gano yadda aka fitar da wasu makudan kudade kimanin naira biliyan 643.8 tare da karin wasu dala biliyan 2.2 ta barauniyar hanya da sunan sayo makaman, tare da dora zargin almubazzaranci kan ofishin Sambo Dasuki.
Kwatsam kuma, a ranar Jummu’ar da ta gabata, mai bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin tsaro- Babangida Monguno ya bayyana cewa an sake handame kudin da gwamnatin tarayya ta were domin sayo makaman, wadanda sun yi ko sama ko kasa.
Ya kada baki ya ce: “Bisa ga hakikanin gaskiya, kudaden da aka yi kasafi don sayo makamai, babu wanda zai gaya maka yadda aka yi dasu.” Wanda idan hakan ya tabbata, kenan an kuma- an maimaita badakalar makamai karo na biyu a Nijeriya, abinda Bahaushe ya ke kira da: ‘Kowane gauta ja ne, sai idan ba a kai shi rana ba.
Mai taimaka wa shugaban kasar, (NSA), Babagana Monguno, ya kara da cewa, wadannan kudin, biliyoyin naira wadanda aka were domin a sayo makamai da albarusai a karkashin tsuffin ahugabin rundunonin sojojin Nijeriya, an rasa inda aka shiga da kudin- ko kasa ko sama. Ya fadi hakan a fira da ya yi da sashen Hausa na gidan radiyon BBC ranar Jummu’a.
Haka zalika ya bayyana hakan yau kimanin wata guda da yan kai da sauya shugabanin rundunonin sojojin Nijeriya da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi tare da maye gurbinsu da wasu sabbi- ranar 26 ga watan Junairun da ya gabata.
Baya ga hakan, gwamnatin APC ta nada tsuffin Hafsoshin makaman jekadun Nijeriya zuwa kasashe daban-daban, wanda daga baya kuma majalisar dattawa ta amince da nadin. Shin hakan ya na nufin an yi batan- bakatantan: babu kuddi kuma babu makamai?
Sannan kuma wannan wani abu mai matukar tayar da tsigar jiki, a matsayin Monguno, wanda tsohon Manjo-Janar ne a gidan soja, ace ya bankado wannan badakalar bayan nada wadannan sabbin shugabanin rundunonin sojojin Nijeriya, wanda ba karamar hujja ba ce wadda babu zancen kokwanto a ciki. Sannan a bayanin nasa, ya nuna cewa ba yana kokarin ya soki tsuffin shugabanin sojojin ba ne, face ya kafe a kan cewa har yanzu babu wanda ya san inda wadannan kudin su ka yi batan dabo.
“Wanda a halin da ake ciki shugaban kasa ya nada sabbin shugabanin sojojin, wadanda ana kyautata musu zaton su yi abin azo a gani. Amma fa ba ina cewa tsuffin shugabanin sojojin ne su ka karkatar da kudin ba, face kawai kudin sun bata, kuma ba mu san inda aka shiga dasu ba.”
Ya kara da cewa, “Amma ko shakka ba na yi shugaban kasa zai yi cikakken bayani kan matsalar. Kuma maganar da nake yi yanzu, ita ma kungiyar gwamnoni a matse take ta san inda kudin suka shiga, kuma ina kara tabbatar da cewa ko shakka babu shugaban kasa zai dauki wannan matsala da muhimmanci tare da bin bahasin lamarin.”
“Har wala yau kuma, matakin farko na bincike ya nuna cewa kudin sun bata, wanda kuma babu maganar makaman ballantana a gansu wani waje. Haka suma bayan nada sabbin shugabanin sojojin, sun nemi makaman kaura-wambai ba su ga komai ba.”
Cikin watan Fabarairun shekarar da ta gabata, an fuskanci yar tsama tsakanin mai bai wa shugaban kasa shawara kan karkar tsaro (NSA) Babagana Monguno da Hafsan sojojin Nijeriya Tukur Buratai a takaddamar da ta kunno kai tsakanin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, marigayi Abba Kyari, da Monguno.
A hannu guda, ko ya yan Nijeriya za su kalli wannan sabuwar badakalar karkatar da kudaden makamai a gwamnatin APC daya yake da na tsohuwar gwamnatin PDP ko ya ya, sannan ya tasirinsa a zabe mai zuwa?
A wata daban, ganin yadda bayanin ke son tayar da balli, Babangana Monguno ya fitar da sanarwa tare da nisantar da kansa da jingina laifin handame kudin ga tsuffin Hafsoahin sojojin Nijeriya, inda ya ce an yi wa bayanin nasa zankam da yi masa bahaguwar fahimta. Ya kara da cewa, “Kuma shugaban kasa ya na bin hanyoyin da su ka dace dangane da wadannan kwangilolin da aka bayar na sayo makamai ga sojojin Nijeriya.”
Shima a nashi bangaren, mai taimaka wa shugaban kasa ta fannin yada labarai, Malam Garba Shehu ya bayyana cewa wadannan kudin ba za su bata ba, ya ce saboda gwamnatin APC ba irin ta PDP ba ce.