Ku Bai Wa ’Yan Nijeriya Tsaro – Sanata Lawan Ga Afrika Ta Kudu

Dattawa

Daga Muhammad Awwal Umar

 

Shugaban majalisar dattawa, Dakta Ahmad Lawan ya bukaci hukumomin kasar Afirka ta kudu da su baiwa ‘yan Najeriya baki mazauna kasar tabbacin bada kariya a wuraren kasuwancin su da ke kasar.

Lawan ya yi wannan kiran ne a lokacin da tawagar mutune uku karkashin jagorancin jakadan kasar ta Afirka ta kudu a Najeriya, Mr. Thamsanga Dennis Mseleku, ta kai masa ziyara a Abuja. Inda ta samu rakiyar Mista Bobby J. Moroe da kuma Misis Boipelo Lefatshe.

A cewar shugaban majalisar, kokarin kasashen biyu wajen bada tsaro ga kasuwancin ‘yan kasashen zai samar da kyakykyawan yanayin da zai samar da aikin yi ga ‘yan kasashen ya kuma tabbatar da yanayin tattalin arziki mai karfi ga Najeriya da Afrika ta kudu.

Ya ce akwai kamfanonin kasar Afrika ta kudu da suka mai da Najeriya tamkar gidan su, dan cigaban da Najeriya ta ke so ta cim mawa a Afrika ta Kudu.

Lawan yace majalisar za ta cigaba da bada goyon baya ga bangaren zartaswa don ganin an bada cikakken tsaro ga wuraren kasuwancin ‘yan Afrika ta kudu, yana mai kira da kasar Afrika ta kudun da ta tabbatar da hakan ga ‘yan kasuwan Najeriya mazauna can.

Lawan yayi kiran karin hadin kai da aiki tare tsakanin majalisun dokokin kasashen biyu da zai amfani nahiyar Afrika baki daya.

Ya yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari da takwaran sa na Afrika ta kudu a bisa matakan da suka dauka na gyara dangantakar kasashen biyu da tayi tsami a lokacin baya.

Ya ce, ya zama wajibi ga kasashen biyu su cigaba da tabbatar da kyakykyawar dangantakar su saboda cigaban nahiyar Afrika.

Exit mobile version