Ku Bamu Varane Mu Baku De Gea

Rahotanni daga ƙasar sipaniya sun bayyana cewa mai koyar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United, Jose Mourinho ya amince cewa zai siyarwa da Real Madrid mai tsaron ragar ƙungiyar, Daɓid De Gea idan har sun amince zasu basu Rafael Ɓarane.

Kusan shekaru uku kenan ajere De Gea yana zama mai tsaron ragar dayafi kowanne ƙoƙari a gasar firimiya ta ƙasar ingila wanda hakan yake nuna har yanzu babu kamarsa a gasar ta firimiya.

A shekara ta 2015 mai tsaron ragar takusa komawa Real Madrid din sai dai an samu matsalar inji wanda yasa takardun De Gea basuje hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya a kan lokaci ba domin ta amince da cinikin.

Ɗan wasan yabuga wasanni 15 a ƙungiyar a halin yanzu a wannan kakar kuma daga ciki ba’a zira masa ƙwallo a raga ba a wasanni 8 a ƙungiyar ta United.

An ruwaito cewa United din zata iya amincewa da cinikin mai tsaron ragar tata inda Real Madrid ta amince zata saka Ɓarane acikin cinikin.

Mourinho dai yanason aiki da Ɓarane saboda shine yasa aka kawoshi ƙungiyar lokacin yana koyar da yan wasan ƙungiyar a shekara ta 2013 daga Nice ta ƙasar faransa.

Watanni 18 kawai yaragewa De Gea a ƙungiyar ta Manchester United sai dai wataƙila zai iya sake sabuwar yarjejeniya da ƙungiyar kafin ƙarshen wannan kakar.

De Gea dai yakoma Manchester United daga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Atletico Madrid a shekara ta 2011 akan kudi fam miliyan 16 lokacin da yake da shekara 18 a duniya.

Exit mobile version