Connect with us

MANYAN LABARAI

Ku Dinga Baiwa Masu Rauni Daga Hatsari Ko Harbin Bindiga Kulawa –Hukumar ‘Yan Sanda

Published

on

Hukumar ‘Yan sandan jihar Barno ta gargadi asibitoci da su dinga bai wa wadanda suka yi hatsari ko harbin bindiga kulawa ko da basu da takardar umarni daga jami’an ‘yan sanda ba, lokaci ne da yakamata hukumar ‘yan sanda ta jawo hankalulan asibitoci kan wannan dabi’ar da take da hatsari.

 

‘Hukumar ta sha nanata wannan cewa, asibiti baya bukatar takardar umarni daga wajen kafin ya aiwatar da aikin shin a ceto ran wadanda aka harba ko hatsari ya rutsa da su, muna rokon duk ma’aikatan lafiya da su kiyaye hurumin rayukan ‘yan adam ta hanyar basu kulawar da ta dace da zarar an kawo su asibiti ba sai an jira wata takardar umarni ba.’ Inji Edet Okon jami’an hulda da jama’a a hukumar.

 

Okon ya kara da cewa: duk da yakamata a daidai lokacin da ake kokarin ceto ran wanda aka harba ko hatsarin mota ya rutsa da shi a sanar da jami’an ‘yan sanda, saboda bin diddigin mai ya faru da daukar matakin da ya dace cikin gaggawa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: