Ku Gaggauta Yin Murabus Cikin Ruwan Sanyi, Akpabio Ya Fada Wa Saraki Da Dogara

Sanatan da ke wakiltar mazabar Arewa Maso Yammacin Akwa Ibom, Godswill Akpabio ya shaida cewar rashin iyawa da rashin yin abun da ya kamata da shugaban majalisar dattawa,  Bukola Saraki da Kakakin majalisar dattawa suka nuna a lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke gabatar da kasafin kudi 2019 abun kaico ne da kuma ya kamata su yi murabus kawai.

Ya bukace su da su yi murabuns cikin ruwan sanyi ba tare da bata wani lokaci ba.

Mista Akpabio ya shaida hakan ne a ranar Laraba, sa’ilin nan da yake ganawa da ‘yan jarida jim kadan bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin na shekara mai zuwa ta 2019 a gaban majalisar kasa da ke Abuja.

Shugaban majalisar dattawa Saraki, da Kakakin majalisar tarayya  Dogara, an yi tsammanin za su sa a yi addu’a gabanin da kuma bayan gabatar da kasafin kudin, amma ba su yi ba, sannan sun gaza gabatar da jawabansu a lokacin da ake gabatar da kasafin na shekara mai zuwa.

Da yake tsokaci kan wannan matakin, tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, ya shaida cewar Mista Saraki da Dogara, sun gaza yin maganar ne a dalilin rashin nagartarsu a halin yanzu, kasancewarsu a bangaren jam’iyyar da ke da rashin rinjaye a majalisunsu.

A cewarsa, “Ba za su iya ba, kuma bai kamata su ci gaba da zama kan kujerunsu ba, tun da yanzu sun kasance a jam’iyyar marasa rinjaye a cikin majalisun nan,” In ji shi.

“A lokacin da nake cikin jam’iyyar marasa rinjaye, nine jagoran marasa rinjaye, amma bai yiwu min na zama shugaban majalisar dattawa ba. Don haka tun da shugabanin sun kasance a jam’yyar marasa rinjaye sai su ajiye kujerunsu su baiwa masu rinjaye zarafin ci gaba da shugabantar majalisun biyu.

“Na yi tsammanin abun da ya faru yau (ranar Laraba) zai sanya mu kiran yi Shugaban majalisar dattawa da Kakakin majalisar Tarayya da su yi murabus cikin ruwan sanyi domin wanzar da zaman lafiya,” ya shaida.

Ya shaida cewar wannan matakin ya haka yake a duniyance, a duk lokacin da ‘yan majalisun da suke da rashin rinjaye ba zai yiwu musu su shugabanci majalisar ba, don haka ne ya yi bayanin cewar dole ne Dogara da Saraki su yi murabus daga kujerunsu cikin sauki.

Ya ke cewa, “Amma za ku iya lura a lokacin da jam’iyyar da ke da rinjaye, APC, ta nuna karfinta. don haka a hankalce, mu mun nutsu mun kasance a nutse lokacin da shugaban kasa ke gabatar da bayani. amma sauran jam’iyyun kuma sun ci gaba da gabatar da sha’aninsu na siyasa,” Inji Sanatan

Sanatan ya shaida cewar kasafin kudin da shugaban shugaban ya gabatar zai bayar da damar farfado da muhimman ababen ci gaban kasar nan.

“Abun farin ciki kan kasafin kudin 2019 da shugaban kasa ya gabatar, akwai kyakkyawar fatar cewar hakan zai farfado da aiyukan da aka lalata a Nijeriya, sannan Nijeriya za ta ci gajiyar wannan kasafin ta fuskacin farfado da muhimman aiyuka.

“Na yi imanin cewar ‘yan Nijeriya za su yi alfahari da kasafin kudin da shugaban kasa ya gabatar domin gwamnatin Buhari tana da zimmar kawo sauyi da cire Nijeriya daga cikin ukuba domin yin aikin da yaranmu za su more nan gaba a fadink asar nan,” Inji shi

Kamar yadda yake fadi, cewar shugaban kasa Buhari ya samu damar yin aiki da kashi 70 zuwa 78 cikin dari na kudin da aka yi amfani da su.

“Wannan bai taba faruwa a karkashin gwamnatin PDP ba, wanda bai wuce kashi 23 cikin dari na manyan aiyukan suke aiwatar ba, amma yau ku duba manyan aiyuka kuma muhimmai da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu nasarar aiwatarwa,” A cewar Sanatan.

Godswill Akpabio ya kara da cewa, “Irin wadannan muhimman aiyukan ba su faru a lokutan baya ba, shi ya sanya manyan aiyukan raya kasar ba su yi kargo ba, kuma ba a iya sarrafa kudaden domin kula da aiyukan da aka samar ba,” Inji shi

Tsohon gwamnan, ya misalta kasafin kudin shekarar mai zuwa a matsayin kasafin da aka gabatar cikin nasara da kwanciyar hankali, yana mai shaida cewar shugaban kasa ya yi kokari wajen shigar da kowace yanki a cikin kasafin, inda ya jinjina masa kan hakan.

Ya shaida cewar kasafin na 2019 zai bayar da damar kyautata rayuwar ‘yan Nijeriya da kuma yin tsarin da kowace yanki za su mori kasafin da shugaban kasar ya gabatar.

Exit mobile version