Connect with us

RIGAR 'YANCI

Ku Gama Da ’Yan Bindiga Kwata-kwata – Masari Ga Sojoji

Published

on

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya umurci Sojoji da su auka tare da gamawa da dukkanin ‘yan bindigar da suka addabi al’ummomi ta hanyar kisan mutane. Gwamnan ya kara da cewa, sam kada ku bar dayansu ya na numfashi, ku kashe su duka.

Masari yana fadin hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar jajantawa a sansanin ‘yan gudun hijira na Faskari, Kadisau da karamar hukumar Dandume, ta Jihar.

Ya ce akwai bukatar a gama da ‘yan bindigar ne kwata-kwata domin dawowar zaman lafiya a yankin.

“Harshen da ‘yan bindigar su ke iya fahimta kawai shi ne karar bindigar AK 47, don haka a bi masu ta inda su ke iya fahimta kawai.

Ya bai wa ‘yan gudun hijira 4,000 da su ke a sansanin da ke makarantar Firamare ta Faskari da kuma kimanin wasu 800 da su ke a sansanin Dandume, tabbacin cewa gwamnatin Jihar za ta ci gaba da daukar dawainiyarsu ta hanyar ba su isasshen abinci, magani da sauran ababen bukatansu a sansanonin na su.

Ya kuma shaida masu cewa da zaran Sojoji da ‘yan sanda da aka aike a kan ‘yan bindigar sun gama lallasa ‘yan bindigar sun kawar da su daga cikin dazukan, al’ummomin za su koma gidajensu domin ci gaba da ayyukan nomansu.

Da ya ke kara yin Allah wadai da ayyukan ‘yan bindigar, ya kuma bayar da tabbacin zakulo duk abokanan ‘yan bindigar masi kai masu rahotanni da su ke a cikin al’ummomin, wadanda ya ce su ma duk abin da ya sami ‘yan bindigar irin hukuncin da su ma za a yi masu kenan.

Da ya isa sansanin ‘yan gudun hijiran da ke Faskari, shugaban kula da sha’anin kudi na sansanin ya shaida wa Gwamnan cewa sansanin ya gama cika makil da zuwan ‘yan gudun hijira daga Kadisau a ranar 9 ga watan Afrilu.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: