Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya shawarci shugabanin rundunonin sojojin Nijeriya su dauki matakin kara gina kyakkyawar alaka da al’umma; ta hanyar cike gibin da ake dashi wajen samun yarda tsakanin jama’a da jami’an tsaro, a inganta hanyoyin sirri wadanda sojoji ke amfani dasu wajen samun bayanan da su ka dace, inda ya bayyana cewa wadannan su ne matakan nasara a yakin da a ke ciki na matsalar tsaro.
Gwamna Zulum ya bayyana hakan a sa’ilin da yake yi wa sabbin shugabanin rundunonin sojojin Nijeriya, a ziyarar su ta farko da su ka kai wa gwamnan ranar Lahadi, a fadar gwamnatin jihar da ke Maiduguri tare da yin kira gare su da cewa, akwai bukatar samun cikakken hadin kan sojojin kasashen makobta irin su Chadi, Kamaru da jamhuriyar Nijar a yaki da Boko Haram.
Sabbin Hafsoshin sojojin, sun kai ziyarar farko a jihar Borno- biyo bayan nada su a makon da ya gabata, wanda jihar ita ce cibiyar yaki da Boko Haram a arewa maso gabashin Nijeriya.
Har wala yau kuma, Gwamna Zulum ya kara bai wa shugabanin sojojin tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bai wa sojojin Nijeriya cikakken goyon baya, a kokarin da suke yi a yaki da suke ci gaba da yi.
Haka kuma, Zulum ya bukaci su rungumi juriya da danne zuciya a korafe-korafen da wasu ke yi, wanda mafi yawan wasu yan kasa suna hakan ne da kyakkyawar niyya tare da zaburar dasu wajen ribanya kokarin da suke yi.
“Saboda a yanayin tsarin mulkin dimukuradiyya, sanannen abu ne ga jami’an sojoji wajen jure muhawara tare da sukar da yan kishin kasa suke yi.”
“Saboda haka, ana kyautata zaton karbar irin wadannan muwara, wadda ake yin ta bisa kyakkyawar manufa tare da burin zaburarwa domin gudanar da ayyukan ku cikin tsanaki.” In ji Zulum.
Bugu da kari, Gwamnan ya shaidar da cewa, sannan domin sojojin Nijeriya su samu nasara a yakin da ake ciki, zai yi kyau a kara jan damara wajen samun cikakken hadin kai tsakanin kowane bangare daban-daban na jami’an tsaron Nijeriya, musamman tsakanin dakarun sojojin kasa da na sama.
A hannu guda kuma, Gwamna Zulum ya yi kira ga sojojin da cewa su dauki ingantattun matakan ci gaba da kai farmaki a maboyar yan ta’adda babu kakkauta wa tare da dakile duk kafar da za za ta bai wa Boko Haram numfashi da hana su rawar gaban hantsi, har su nemi mashiga ko mafaka su rasa.
A nashi bangaren, shugaban tawagar Hafsoshin sojojin, kuma shugaban ma’aikatan shalkwatar tsaro ta Nijeriya, Manjo Janar Leo Irabor ya lashi takobin cewa zaratan sojojin sa za su dauki sabbin matakan kai farmaki ga maboyar yan ta’addan babu kakkauta wa har sai sun ga bayansu baki daya. Haka kuma ya ce rundunar sojojin za ta dauki matakan sake farfado da fahimtar al’umma a yakin da take da matsalar tsaro.