Ku Shirya Jin Radadin Karin Farashin Fetur –Ministan Mai Ga ’Yan Nijeriya

Farashin Mai

Karamin ministan albarkatun mai, Cif Timipre Sylba ya tunatar da ‘yan Nijeriya cewa, su shirya jin radadin karin kudin man fetur tun da dai gangan kowacce danyan mai ya kai dala 60. Ministan ya bayyana hakan ne lokacin da yake yin jawabi wajen kaddamar da shirin farashin mai a wajen sarin mai wanda ya gudana a ranar Talata. Sylba ya bayyana cewa, sakamakon babu wani tallafi a cikin kasafin kudin shekarar 2021, kamfanin mai ta kasa (NNPC) ba za ta ci gaba da sayar da mai a yadda take sayarwa ba.

A yanzu haka dai, ana sayar da man kan naira 160 zuwa 165 a kan kowacce lita daya, an saka wannan farashin ne lokacin da gangan kowacce danyan mai take kan dala 43 a kasuwan duniya tun watanni hudun da suka gabata.

A cewar ministan, a dai-dai lokacin da gwamnatin tarayya take kokarin samun kudaden shiga daga farashin danyan bai, zai kuma yuwuba ta ci gaba da biyan tallafin mai a cikin kasar nan.

Ya ce, “dun da dai a halin yanzu muna kokarin inganta komi ne, dole ne akwai bukatar kamfanin NNPC ya yi tunanin inganta farashin man fetur saboda mun san dukkanin yadda farashin danyan mai a yanzu yake wanda ya kai dala 60 ga kowacce gangan mai a kasuwan duniya.

“Sakamakon faruwar wannan lamari wanda ya kyawaye bangaren mai, wannan ba kara min matsala da a samu ba a cikin farashin mai. Domin haka ne, muke sanar wa ‘yan kasa cewa, su shirya jin radadin karin farashin mai wannan za a fuskanta a nan gaba.

“A yau kamfanin NNPC ya samu babban gibi wanda ba zai ci gaba da gudanar da ayyukan kamar na shekarun baya ba. Kamar yadda muka sani babu kudaden tallafi a cikin kasafin kudi na wannan shekara.

“Domin haka, a karkashin wannan lamari, na tabbatar da kamfanin NNPC ba zai taba ci gaba da daukar kasada ba kamar yadda ya dauka a shekarun baya, saboda a yanzu abubuwa sun canza. Babu wata hanya da za a bayar da tallafin man fetur a cikin kasar nan a halin yanzu.

“Nijeriya a matsayinta na kasa, za mu fuskanci hauhawar farashin danyan mai wanda a hakan za mu iya amfana, ina fatan za mu shirya jin radadin karin farashin mai a cikin kasar nan,” in ji shi.

Sakamakon yadda gangan danyan mai ya kowa a kasuwan duniya ne ya sa minista ya gudanar da wadannan bayanai wanda ana kayyade farashin mai yadda kasuwan dunaya ta kama. Manyan kungiyoyin ‘yan kasuwan guda biyu sun bayyana wa manema labarai cewa, farashin mai zai ci gaba da karawa idan ba gwamnatin tarayya da dawo da zamanin bayar da tallafin mai ba.

Exit mobile version