Ku Yi Amfani Da Damar Da Arewa-maso-Yamma Ta Samu Na Karfafa Nasarar Ci Gaba - Fall
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ku Yi Amfani Da Damar Da Arewa-maso-Yamma Ta Samu Na Karfafa Nasarar Ci Gaba – Fall

byMuhammad and Leadership Hausa
1 year ago
Arewa

Yayin da Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma da Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya ke yunkurin tabbatar da dorewar zaman lafiya a yankin, babban jami’in kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya.

Mohamed Malick Fall, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su yi amfani da damar da yankin Arewa-maso-Yamma ya samu masu yawa ta hanyar karfafa nasarar cimma muradun ci gaba mai dorewa (SDGs) da kuma kafa hanyar samar da ci gaba na dogon lokaci da magance matsalolin al’ummar yankin.

  • Babu Mai Faɗa Maka Matsalar Tsaro Daga Amurka Fiye Da Wanda Abin Ya Shafa – Radda
  • Tsaro: Gwamnoni Arewa Maso Yamma Za Su Yi Taro Domin Neman Mafita A Katsina

    “Bari mu kuma shiga cikin babbar damar da yankin ke da ita don karfafa nasarorin da aka samu na SDGs da kuma kafa hanyar samar da ci gaba mai dorewa a yankin. Mu zabi ba da fifiko wajen daidaita rarrabuwar kawuna da haduwar juna don bunkasa dabi’un hakuri da mutunta juna da sulhu da mutuncin dan Adam.”

Ya bayyana hakan ne a taron farko na zaman lafiya da tsaro na yankin Arewa maso Yamma da ke gudana a ranakun 24 zuwa 25 ga watan Yunin 2024, a Katsina.

Fall ya lura cewa, don magance kalubalen da ake fuskanta a yankin Arewa maso Yamma yadda ya kamata, zai bukaci hanyoyin da za a bi a fannoni daban-daban a fannin ayyukan jin kai, ci gaba da gina zaman lafiya, wannan, a cewarsa, “Zai ba mu damar karfafa matakan tsaro ta yadda za a magance matsalolin da suka addabe su kamar karancin albarkatun kasa, magance zurfafa rashin daidaiton tattalin arziki, da magance rarrabuwar kabilanci da addini wadanda dukkansu ke da tushe.”

Ko’odinetan ya jaddada cewa, ya kamata mu mai da hankali wajen inganta harkokin gudanar da mulki tare da tabbatar da adalci, ilimi, samar da walwala, inda ya ce ta hanyar inganta huldar da ke tsakanin gwamnati da ’yan qasa, ita ce babbar yarjejeniya ta zamantakewa. Za mu iya ganin waxannan tsare-tsaren suna canzawa ta hanya mai dorewa don ciyar da ajandar zaman lafiya a Nijeriya.

“A yau mun kuduri aniyar daukar matakan samar da zaman lafiya wanda zai ciyar da ajandar SDG gaba, da kuma gina Nijeriya wanda hakan zai bai wa kowa damar gudanar da ‘yancinsa da cikakken iko.
Majalisar Dinkin Duniya tana goyon bayan Nijeriya a kokarinmu na hadin gwiwa don tallafa wa daidaito, ‘yancin dan adam da wadata ga kowa da kowa,” a cewar Fall.

Taron mai taken “Haɗin Kai Tsakanin Yankuna Don Tabbatar Da Rayuwa Da Walwala A Yankin Arewa Maso Yammacin Nijeriya,” ya samu halartar Mataimakin Shugaban Kasar Tarayyar Nijeriya Sanata Kashim Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A jawabinsa na musamman, Shettima ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta qaddamar da shirin sake mayar da jama’ar Pulaku muhallinsu a matsayin wani shiri na kishin kasa domin magance wasu matsalolin da ke haifar da rigingimu da rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma.

“Za a fara aikin gwajin ne a Jihohin Sokoto, Kebbi, Benue, Katsina, Zamfara, Neja da Kaduna”. Shettima ya jaddada cewa, “Sakamakon shirin ya hada da gina gidaje, tituna, makarantu da muhimman ababen more rayuwa, wanda ke nuni da kudurin gwamnati na samar da ci gaba mai dorewa da kuma dunkulewar kasa, lumana da wadata Nijeriya.”

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa Maso Yamma kuma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya jaddada muhimmancin hadin kan yankin wajen magance matsalar rashin tsaro. Ya kuma bayyana kokarin kungiyar gwamnonin Arewa maso Yamma wajen magance matsalolin da suka hada da tsaro, noma, da samar da wutar lantarki.

Gwamna Radda ya bayyana cewa, “Gwamnonin sun kaddamar da wasu tsare-tsare na tsaro a jihohinsu, kamar kungiyar Community Watch Corps da ke Katsina, domin yin aiki tare da jami’an tsaro.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu
Siyasa

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya
Manyan Labarai

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace
Labarai

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Next Post
Peng Liyuan Da Uwargidan Shugaban Poland Sun Ziyarci Cibiyar Gabatar Da Wasannin Fasahohi Ta Sin

Peng Liyuan Da Uwargidan Shugaban Poland Sun Ziyarci Cibiyar Gabatar Da Wasannin Fasahohi Ta Sin

LABARAI MASU NASABA

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version