Daga Hussain Baba, Gusau
Rundunar’yan sandan Jihar Zamfara ta samu nasarar gano jami’anta da aka sace a garin Keta da ke cikin Karamar Hukumar Tsafe. Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Zamfara, Shaba Alkali ne ya tabbatarwa da manema labarai haka a ofishinsa da ke Gusau, ranar Asabar 16 ga Satumbar, 2017.
‘yan sandan dai an sace su ne da tsakar ranar Litinin 5 ga watan Satumbar 2017, inda wasu mahara da suka haura 20 suka yiwa ofishin ‘yan sanda dake garin Keta dirar mikiya, suka farfasa kayayyakin ofishin, suka yi awon gaba da jami’ai har uku, sannan suka saki dukkanin mutanen da ake tsare dasu a ofishin.
Kwamishinan ‘yan Sandan ya bayyana cewa “Rundunar ‘yan sanda ta yi iyaka kokarinta wurin ganin ta gano wadannan jami’an nata da aka sace.Sunayen jami’an da aka sace, kuma muka samu nasarar kwato su akwai; ASP Ahmad Shehu da Sajant Safiyanu Bara’u da kuma Musa Balarabe.”
Haka kuma ya yi kira ga jami’ansa cewa da zarar sun ga abin da basu gane masa ba, su yi kokari su aika da rahoto domin a iya daukar mataki da gaggawa.