Kudaden Da Ake Karba A Kogin Hadejia Jama’are Daga Hannun Manoma, Ba Haraji Ba Ne - HJRBDA
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kudaden Da Ake Karba A Kogin Hadejia Jama’are Daga Hannun Manoma, Ba Haraji Ba Ne – HJRBDA

byAbubakar Abba and Sulaiman
4 months ago
HJRBDA

Hukumar da ke kula da madatsar ruwa ta Hadejia Jama’are (HJRBDA), ta shaida wa manoma da kuma kungiyar masu yin amfani da ruwan madatsar ta WUA cewa; kudaden da take caza daga wurinsu, ba matsayin haraji ba ne.

Manoman da kuma kungiyar, na yin amfani da ruwan a shirin aikin noman rani na KRIP da ke Kogin na Kano, wanda ofisnta yake a Karamar Hukumar Kura da ke fadin jihar.

  • An Kaddamar Da Bikin Gabatar Da Jerin Shirye-shiryen Telebijin Da Fina-finai Na CMG A Birnin Astana
  • Gwamnatin Tarayya Ta Himmatu Wajen Inganta Karfin Sashen Fetur Da Gas Na Cikin Gida

A cewar mahukuntan hukumar, ana karbar kudaden ne, domin gudanar da wasu ayyuka na musamman, domin hukumar ta samu damar gudanar da wasu ayyukanta da kuma kara inganta kayan aiki, na noman ranin.

Shugaban hukumar na HJRBDA, Rabiu Suleiman Bichi, ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar rangadi a wasu Dam-dam da ke aiki da wutar lantarki, wadanda kuma suke a karkashin kulawar hukumar.

Rabiu ya bayyana cewa, hukumar ta mayar da hankali wajen ganin tana kara bunkasa ayyukanta tare kuma da ci gaba da kula da sauran manyan kayan gudanar da ayyukanta da kuma ci gaba da taimaka wa manoman, domin su samar da wadataccen abinci da kara habaka tattalin arzikin da ke yankin.

Ya kuma bukaci da a ci gaba da hada hannu da masu ruwa da tsaki a fannin, musamman domin dakile kalubalen da ake fuskanta na rashin amfana da albarkatun da ke madatsar ruwan, musamman domin kara bunkasa fannin aikin noma da kuma kara samar da wadataccen abinci.

A nasu martanin daban-daban, wasu daga cikin manoman sun yi kira ga hukumar ta HJRBDA, da ta samar musu da Taraktocin noma a daminar bana da kuma lokacin noman rani.

Tawagar ta hukumar HJRBDA, ta ziyarci wuraren adana ruwa; ciki har da na Challawa, Dam din Gorge, wanda ke adana ruwa mai karfin tsawon zurfin mita miliyan 962 da Dam din Tiga, wanda ke iya adana ruwan da zurfinsa ya kai kimanin mita biliyan 1.968 da madatsar ruwan ta Ruwan Kanya da ke iya adana ruwan da ya kai zurfin mita miliyan 50.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina
Noma Da Kiwo

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina

October 3, 2025
Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo
Noma Da Kiwo

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo

October 3, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi

September 27, 2025
Next Post
Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Addu’ar Kwana 3 Don Samun Isasshen Abinci

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Addu’ar Kwana 3 Don Samun Isasshen Abinci

LABARAI MASU NASABA

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version