Abubakar Abba" />

Kudin Ajiyar Nijeriya Na Kasashe Waje Ya Ragu Zuwa Dala Biliyan 42.86 A Cikin Wata Biyu

Bayanan da aka samo na kwanan daga Babban Bankin Nijeriya CBN ya nuna cewar, kudin ajiyar Nijeriya na kasar waje ya ragu zuwa dala biluyan 42.86, inda hakan ya nuna cewar ya ragu sosai a cikin watanni biyu.
Bayanan wanda aka samo a ranar Lahadin data gabata sun nuna cewar, kudin ya kai dala biliyan 43.174 a ranar 31 ga Janairu, India suka ragu zuwa dala miliyan 314 a cikin sati biyu kuma suka ragu zuwa dala biluyan 42.86bn a ranar 14 ga Fabarairu.
Kudin kuma haura zuwa dala biliyan 47.865 a ranar 10 ga Mayun 2018, amma kuma suka kara raguwa zuwa dala biliyan 41.523 a ranar 22 ga Disamba.
Har ila yau, a ranar 13 ga Disamba, kudin sun kai dala biliyan 42.877.
Acewar sabon rahoton PwC Nigeria, mai taken, “ Hangen Tattalin Arzikin Nijeriya na manya 10 na shekarar 2019’, Babban Bankin Nijeriya ya kara zuba dala a kasuwar sayar da hannun jari ta kasa da suka kai kashi 87 bisa dari zuwa dala biliyan 40 a shekarar 2018 a bisa kokarin da bankin take yi na samar da kyakyawar dorewar shirin na musayar kudi.
Rahoton ya ci gaba da cewa, tarihin baya ya bayar da shawarar lokacim gudanar da zabbbuka ne suka janyo samun raguwar kudin da kuma kara nuna bukatun kudin kasar wajen na musaya.
Acewar rahoton, an samu raguwar data kai kashi 24 bisa dari na kudaden ajiyar na kasar waje daga Janairun 2010 zuwa Mayun 2011, inda raguwar ta kai kashi 30 bisa dari daga daga Janairun 2014 zuwa Mayun 2015.
Wasu masu fashin baki a Cordros Capital a ranar Juma’ar data gabata sun bayyana cewar, kudin ajiyar sun ragu a cikin satin biyu, ganin cewar, Babban Bankin Nijeriya CBN ya kara samun kudin ajiyar sun sauna zuwa dala miliyan 88.07 daga sati zuwa sati zuwa dala biliyan 42.86.
Sun bayyana cewar, jimlar masu zuba jari da kuma masu fitar da Maya zuwa kasashen waje sun ragu zuwa kashi 38 bisa dari, inda kudin suka kai raguwar dala biliyan 1.03.
Naira ta samu yar darajar da ya kai kashi 0.02 bisa dari zuwa naira 361.65 akan dala, inda kuma ragin ya kai kashi 28 bisa dari zuwa naira 362 akan dala a kasuwar bayan fage.
A kasuwar dala da kuma naira sun kara samun daraja a daukacin dukkan kwangiloli a cikin watanni uku, inda suka kai kashi 0.11 bisa dari zuwa naira 370.68, haka a cikin watanni shida sun kai kashi 0.14 bisa dari zuwa naira 382.26, inda kuma a cikin shekara daya, sun kai kashi 0.03 bisa dari zuwa naira 412.11 da aka kebi a gu guda a wata daya da ya ragu zuwa kashi 0.08 bisa dari zuwa naira 368.24.

Exit mobile version