Connect with us

RAHOTANNI

Kudin Korona: Majalisa Ta Gayyaci Ministar Tallafi Da Jin Kai.

Published

on

Kwamiti Na Majalisar Wakilai Mai Kula da kudin kasa ya gayyaci ministar jinkai da tallafi, Hajiya Sadiya Umar Faruk, da ta bayyana yadda ta rarraba kudin tallafin korona da kwamitin shugaban kasa ya bayar ga Ofishinta da hukumomin dake karkashinta

Kwamitin ya nemi ta bayyana agabanshi Ranar Alhamis Mai zuwa don yin bayani, kuma za a tambayeta game da yadda ake gudanar da harkar N-power da sauran tsare-tsaren tallafi na shugaban kasa da yakawo.
Kwamitin yayi matukar ji-mami da yadda shuwagaban nin N-power, Masu bada tallafin korona na gaggawa, da wadanda tsarin ciyarwa na ‘yan makaranta ke hannunsu, sukaki yarda da su bayyana agaban kwamitin don yin bayanin yadda sukayi aiki da kudaden da aka basu.
Shugaban Kwamitin wato Wole Oke, ya bada umarni ga wadanda abun ya shafa da su bayyana gabanshi Ranar Alhamis. Kin Bayyana a yadda yace zai basu dama na kamo duk wanda yaki zuwa.
Ya kuma kara bada wani umarni ga shugaban bincike na kasa da ya bayyana sakamakon ayyukan wadannan hukumomi da jajircewarsu wajen ayyukansu yayin kulle da akayi don Korona.
A wani qarin bayani kuma, shugaba mai kula da safarar yara, wato Julie Okah-Doni ya bayyana gaban kwamitin a ranar Talatar data wuce yana bayyana cewa hukumar tasa ta ruwaito kusan tashin-hankula guda hamsin aciki harda fyade a yayin kulle da akayi don Korona
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: