Kudin Makamai: Kotun Daukaka Kara Ta Wanke Shekarau

Kudin Makamai

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Kano ta wanke Sanata Malam Ibrahim Shekarau daga zargin aikata laifukan da Hukumar EFCC ke yi ma sa, wadanda su ke da alaka da kudin da a ke yi mu su lakabi da ‘Kudin Makamai’.

Laifukan kuwa su ne, hada baki da wani Injiniya Mansur Ahmad, don aikata laifuka da karbar Naira miliyan 25 ba ta hanyoyin da su ka halasta ba da kuma ajiye Naira milyan 950 a gidansa; kudaden da a ka karbo daga wurin tsohuwar Ministar Albarkatun Man Fetur, Dizani Alison Maduekwe, inda a ka yi zargi Shekarau ya amince a raba wa ’ya’yan jamiyyar PDP a Jihar Kano a gidansa, don yin amfani da su a zaben shekarar 2015.
A yayin da ta ke karanto hukuncin da Mai Shari’a Abubakar Datti Yahaya ya rubuta, wanda Mai Shari’a Amina Wambai ta bayyana, ta ce, ko kadan Hukumar EFCC ba ta gabatar da gamsassun shaidu da hujjojin da za su sa kotu ta cigaba da tuhumar Malam Ibrahim Shekarau ba, balantana ta umarce shi da ya kare kansa.
Idan za a iya tunawa, a ranar 27 ga Satumba 2019 Babbar Kotun Tarayya da ke Kano a karkashin jagorancin Mai Shari’a Lewis Allagoa ta bada ra’ayin cewar, akwai alamun gaskiya a zarge-zargen da a ke yi wa Shekarau, inda ta umarce shi da ya fara kare kan shi. A kan haka ne lauyoyinsa su ka daukaka kara.
Kotun daukaka karar ta kuma bayyana cewar, babu kamshin gaskiya ko kuma wata alaka tsakanin Naira milyan 25 da Hukumar EFCC ta ke zargin tsohon Gwamnan Jihar Kano ya karba.
Haka kuma kotun ta bayyana cewa, Hukumar EFCC ta gaza wajen bayar da hujjojin da za su tabbatar da cewar Malam Shekarau ya taka rawa wurin raba wa ’yan PDP Naira miliyan 950 a gidansa, inda ta ce hasalima hukumar ta gaza wurin bayyana cewar, Naira miliyan 950 an debo su ne daga lalitar gwamnati, inda ta ce, bayanai sun bayyana cewa, kudade ne na PDP a wani banki. Kotun ta ce, kamata ya yi EFCC ta gabatar da Maduekwe ne, domin ji daga bakinta.
Ta cigaba da cewa, ita kotu ba ta amfani da jita-jita, sai gaskiya a zahirance. Ta kara da cewa, babu yadda kotu za ta yi illa kawai ta sallami Shekarau, saboda gazawar shaidu da a ka samu daga EFCC.
Barrister Abdul Adamu Fagge na daga cikin lauyoyin Malam Shekarau. Ya yi karin haske dangane da zaman na Talatar nan, inda ya ce, gaskiya ce ta yi halinta, kuma ya gode wa Allah bisa nasarar da Sanata Shekarau ya samu.
Wakilin LEADERSHIP A YAU ta yi kokarin jin ta bakin lauyoyin Hukumar EFCC, amma dole mu ka hakura, domin tun farkon zaman magatakardar kotun ya sanar da uzurin rashin zuwansu kotun.

Exit mobile version