Alkaluman da ma’aikatar masana’antu da sadarwa ta kasar Sin ta fitar, sun nuna daga watan Janairu zuwa watan Afirilun bana, masana’antun samar da manhajoji da ayyukan ba da hidimomin fasahohin sadarwa na Sin sun bunkasa lami lafiya.
Alkaluman sun nuna cewa, daga watan Janairu zuwa watan Afrilun bana, jimillar kudin shiga da masana’antar ta samu, ta haura yuan tiriliyan 4.25, adadin da ya karu da kaso 10.8 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokaci a bara. Kazalika, jimillar ribar masana’antar manhajojin ta kai yuan biliyan 507.5, yayin da saurin karuwar jimillar ribar masana’antun ta yawaita zuwa kashi 14.2 bisa dari.
Har ila yau, jimillar kudin shigar masana’antun fitar da kayayyakin manhajojin ta kai dalar Amurka biliyan 17.26, adadin da ya karu da kashi 3.5 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokaci na bara. (Safiyah Ma)