Rabiu Ali Indabawa" />

Kudirin Dokar Fetur: Yadda Kabilun Neja Delta Suka Dambace A Majalisar Wakilai

An bai wa hammata iska a tsakanin wakilan al’ummomin yankin Neja Delta da ake hada-hadar manfetur a yankunansu, a ranar Alhamis, yayin wani taron jin ra’ayoyin jama’a game da Dokar Sashen Manfetur (PIB) a zauren Majalisar Wakilai.

Rikicin ya barke ne a zauren sauraron korafi da ke daki na lamba 028, tsakanin wasu shugabannin al’ummomin da aka karbi bakuncinsu a majalisar.
Tun da fari, Shugaban Kwamitin da yake sauraron ra’ayoyin jama’ar, Honarabul Mohammed Monguno ya fada a bayaninsa cewa, bayan shugabannin Kamfanin Hostcom sun kammala gabatar da bayanansu, daga baya za a gayyaci sauran shugabannin kabilun da ake karbar bakuncin daya-bayan-daya su gabatar gabatar da nasu.
Kwatsam! jin haka ke da wuya, sai wakilan suka rude da ihu na nuna rashin amincewa suna fadin “a’a, a’a, sam ba za ta sabu ba!”
Fadan ya barke ne daidai misalin karfe 12:10 na rana, a lokacin da Shugaban Kwamitin Riko kan kudirin na PIB, Honarabul Mohammed Monguno, wanda shi ne ke tsara yadda ake gudanar da jin ra’ayoyin jama’ar.
Yayin da ‘yan majalisar suka ga an dambace, sai suka yi ta maza tare da sauran mahalarta zaman, da rikicin bai shafe su ba, suka fara rabo da shiga tsakani ta hanyar sanya baki don kare lafiya da kuma riga-kafin naushe wani har lahira.
Duk da yake ba a san musabbabin dambacewar ba, ga dukkan alamu wadanda suka zama shago a wurin sun isa zauren majalisar ne a kullace da juna.
Cikin bidiyoyin da ke yawo a kafafe daban-daban, an ga yadda wani mai doguwar riga irin ta dattawan yankin Neja Delta ya yi ta kifa wa wani dattijo naushi har sai da ya kai shi kasa.
A bidiyon da gidan talabijin na Channels ya sanya a shafinsa na youtube, an ga dattijon da aka naushen ya tashi baki da jini, sannan an nuno shi yana share baki da wani farin kyalle. Har ila yau an nuno wani farin kyalle yashe a kan kujera da aka share jini da shi aka yar.
A baya, shugaban malisar ta wakilai, Femi Gbajabiamila, ya sha nuna bacin ransa game da gazawar gwamnatocin da suka gabata a kasar wajen tabbatar da dokar PIB ta zama a matsayin doka.
A cewarsa, yana da wahala a bayyana dalilin da ya sa ba a zartar da kudurin ba duk da cewa kowane a cikinsu na da sha’awar samar da kudirin.  Majalisar ta 8 ta sami damar zartar da wani bangare na kudirin bayan ya kasance kashi uku na kudade daban-daban, wato Masana’antar Manfetur, da Dokar Gudanarwa (PIGB), 2016; Dokar Kariya, 2016; da kuma Dokar Kasafin Kudi ta Masana’antar Manfetur.
PIGB da Majalisar Dokoki ta 8 ta zartar, ya sami karbuwa daga Shugaban kasa Muhammadu Buhari. An tura wani kudurin doka ga Majalisar kasa a Satumbar 2020, kuma Majalisar ta zartar da kudirin don karantawa a karo na biyu a watan Nuwamba 2020.
A ranar Laraba, Gbajabiamila ya ce, “Abin takaici ne kuma a fili
mai wahalar bayyana, yadda gwamnatocin da suka gabata suka kasa cika alkawarin kawo gyara duk da wannan yerjejeniyar.
“Na dade, mun san cewa wannan babbar masana’antar ta kasa tana nuna gazawarta da kuma abin da ‘yan kasa za su yi tsammani a kasarmu. Ga mafi yawanci, dukkanmu mun yarda da bukatar aiwatar da doka inganta ta tsarin doka da tsarin mulki.” In ji shi

Exit mobile version