Kudirin Dokar Man Fetur Zai Bai Wa Nijeriya Damar Cin Gajiyar Albarkatunsa – Majalisar Dattawa

Kudurin

Daga Muhammad Maitela,

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan yace kuduri dokar bangaren man fetur, watau Petroleum Industry Bill (PIB) da ke gaban majalisar zata ba yan Nijeriya damar cin gajiyar man fetur da sauran albarkatun da suka shafi masana’antar.

Dr. Lawan ya bayar da wannnan tabbacin ne ranar Litinin yayin da da yake bude taron kwana biyu don jin ra’ayin jama’a dangane da kudurin dokar a Abuja.

Shugaban majalisar ya bayyana hakan a sanarwar namema labarai mai dauke da sa hannun mai taimaka masa kan aikin yada labarai, Mista Ezrel Tabiowo.

A cewar shugaban majalisar, a yayin zauren majalisar ke nazari da aiki akan kudirin dokar, zauren majalisar zai yi kokari wajen tabbatar da cewa bayan zama doka, kudurin zai samar da karin kudin shiga ga kasar nan.

“Allah ya albarkaci Nijeriya da albarkatun kasa masu tarin yawa don haka muna so kasar nan ta amfana da su. Wanda bisa ga hakan ne mu ke aiki tukuru don ganin amincewa da wannan kudurin doka cikin hanzari, wanda saboda rashin dokar a baya ya jawo mun yi asara ta tsawon shekaru da ya kamata mun fara cin ganiyar wannan albarkatun.”

Ya ce, rashin amincewa da kudurin dokar ta PIB ya jawo koma baya ga dangaren man fetur, musamman ta rage sha’awar masu zuba jari a nan cikin kasa tare da na waje a daidai lokacin da wasu kasashe wajen suka aiwatar da ita don habaka albarkatun mai da iskar gas din da suka mallaka.

Ya ce abin kunya ne ace ana amfani da dokokin da aka kafa sama da shekaru 50 da suka wuce wajen gudanar da bangaren harkokin man fetur a kasar nan.

Bugu da kari kuma, ya ce, a matsayin su na masu yin dokoki, za su yi bakin iyawar su domo habaka ci gaban bangaren man fetur da iskar gas, ta hanyar zamanantar da hada-hadarsu, tabbatar da gasa da kirkiro kyakykyawan yanayi ga dukkan masu ruwa da tsaki a bangaren.

Ya kara da cewa, yayin da aka amince da kudurin dokar kuma shugaban kasa ya rattaba mata hannu, hakan zai taimaka wajen inganta rayuwar mai dorewa ga al’ummar da ake hako shi a yankunan su tare da samar masu da abubuwan more rayuwa da habaka tattalin arzikin su.

Lawan ya bayar da tabbacin cewa majalisar dokokin Nijeriya za ta yi amfani da ra’ayoyin jama’a wajen magance duk matsalolin sa suka shafi bangaren man fetur don magance gaggarumar asarar da Nijeriya ta ke yi.

Exit mobile version