Kududdufi Ya Ci Ran Wani Matashi A Kano

Wani matashi mai shekara 20 mai suna Sani Iliyasu ya nutse a cikin kududdufi a yayin da yake wanka a Bachirawa dake Darerawa a karamar hukumar Ungogo a jihar Kano. Jami’in hulda jama’a na hukumar kashe gobara, Malam Saidu Mohammed shi ne ya tabbatar da hakan.

Mohammed wanda ya bayyana hakan a yayin ganawarsa da manema labarai ya ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi a yayin da Marigayin ya je wanka kududdufin.

Ya kara da cewa wani mai suna Malam Abdulrahman Adamu, shi ne ya kira su da misalin karfe 12: 45 ma rana yake shaida musu cewa an samu gawarsa cikin kududdufin tana yawo. Ya ce da misalin karfe 1 jami’ansu suka je suka ciro mamacin.

Ya ce an mika gawarsa ga Mai garin Zangon Barebari, Alhaji Ahmed Isa.

Exit mobile version