Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Kudurori Marasa Kyau Na ‘Yan Siyasar Amurka Suna Jefawa Duk Duniya Cikin Mawuyacin Hali

Published

on

A kwanakin baya ne ‘dan jaridar kamfanin dillancin labarai na Reuters na Birtaniya Shrutee Sarkar ya wallafa wani rahoto, inda ya yi nuni da cewa, “Kafin barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19, Amurka ta taba taka babbar rawa kan ci gaban tattalin arzikin duniya, amma yanzu tana haifar da illa ga karuwar tattalin arzikin duniya.”

A halin yanzu duk da cewa, asusun kota kwana na tarayyar Amurka ya yi alkawari cewa, zai dauki dukkan matakan da suka wajaba domin raya tattalin arzikin kasar, amma bai cimma burinsa ba. Kwanan baya, darajar dalar Amurka ta fadi, kuma daga watan Maris zuwa yanzu, adadin mutanen da suka rasa aikin yi a kasar ya zarta miliyan 51, kana adadin GDP na kasar a rubu’i na biyu ya ragu da kaso 32.9 cikin dari, mafi muni a tarihin kasar tun bayan shekarar 1947, tashar yanar gizo dake wallafa labaran siyasar kasar wato Politico ta ruwaito sakamakon binciken kamfanin cinikayyar musanyar kudi na Oanda cewa, a bayyane an lura cewa, adadin GDP na kasar a rubu’in ya kunyata kasar Amurka.
To mene ne dalilin da ya sa haka?
Kamar yadda wasu masu sharhi kan al’amuran yau da kullum suka bayyana cewa, kuskuren gwamnatin Amurka ta yanzu abin dariya ne, har ma ta siyasantar da kwayar cuta, abun bakin ciki shi ne, kudurori da ba su dace ba da gwamnatin Amurka ta tsai da a jere, suna jefa daukacin kasashen duniya cikin mawuyacin hali.
A bangaren dakile annobar kuwa, ba ma kawai Amurka ta ki amsa alhakin abin da ta aikata ba, har ma tana kawo cikas kan tsaron lafiyar jama’a, abun mamaki shi ne ta fice daga hukumar lafiya ta duniya a wannan lokaci na musamman.


A bangaren tattalin arziki, Amurka tana kawo hadari ga farfadowar tattalin arzikin duniya, saboda koma bayan tattalin arzikin Amurka zai kawo cikas kan ci gaban tattalin arzikin duniya, a sa’i daya kuma, Amurka tana rage cudanyar tattalin arziki dake tsakaninta da sauran kasashen duniya sakamakon mummunan yanayin kasuwanci.
Duk wadannan alamu sun nuna cewa, kudurori marasa kyau da wasu ‘yan siyasar Amurka suka tsai da suna jefa kasar kanta da daukacin kasashen duniya cikin yanayi mai tsanani.(Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)
Advertisement

labarai