Khalid Idris Doya" />

Kujerar Sanatan Bauchi Ta Kudu: Yadda APC Ta Samu Nasara Ba Tare Da Dan Takara Ba

A daidai lokacin da al’umma a Nijeriya suke kan sauraron sakamakon wadanda suka yi nasara bayan gudanar da zaben ranar Asabar. A jiya Talata ne aka ayyana jam’iyyar APC ce ta samu nasarar lashe kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu, kamar yadda jami’in tattaka sakamakon zaben wannan kujerar Farfesa Ahmed Sarkin-Fagam ya ayyana, ya ayyana cewar APC ta samu nasara amma babu dan takarar da ya bayyana a matsayin wanda shine ya dale kujerar.

Da yake sanar da sakamakon zaben a ofishin INEC da ke Bauchi, Farfesa Ahmed Sarkin-Fagam wanda malami ne a jami’ar Abubakar Tafawa Balewa Unibersity (ATBU), Bauchi, ya shaida cewar APC ta samu nasarar ne da kuri’u 250,725, wanda hakan ya bata damar dara wa sauran jam’iyyun, sai dai kuma fa, ya ce babu wani sunan dan takara takamaimai da ke kan wannan kujerar kawo yanzu, a saboda umurnin da wata kotu ta bayar kan Sanata Lawan Gumau da ke cewar ba shine ya cancanci zama a kan kujerar ba.

Farfesan ya ci gaba da bayyana sakamakon dacewar dan takarar jam’iyyar PDP Alhaji Garba Dahiru, ya samu kuri’u 175,527, a yayin da kuma dan takarar jam’iyyar PRP Lawal Ibrahim ya tashi da kuri’u 43,386 a kan wannan kujerar.

Jami’in tattara sakamakon ya bayyana cewar jam’iyyu guda 18 ne suka tsaya neman wannan kujerar a wannan mazabar, wanda dukkaninsu APC ta kayar da su.

Ya yaba wa Kwamishinan INEC a jihar Bauchi, Alhaji Ibrahim Abdullahi, a bisa cikakken bayanin da yayi na cewar APC ta kaza samar da dan takarar da yayi nasara ne a sakamakon umurnin da wata kotu ta bayar kan dan takarar mazabar a wannan jam’iyyar.

Kamar yadda yake shaidawa, Sanata Lawan Gumau wanda yanzu haka yake kan kujerar, kana ya samu dalewa kujerar ne bayan da ka yi zaben cike gurbi a kwanakin baya, ya samu tarnakine bayan da wata kotu ta yanke hukuncin da ke cewar ba shine dan takarar wannan kujerar ba.

Don haka ne ya shaida cewar a daidai wannan lokacin jam’iyyar babu dan takara, amma dai ita ce ta samu nasara, don haka ne Gumau bai kasance wanda ya samu nasarar sake dawowa kan kujerar ba kawo yanzu.

Kujerar majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Bauchi ta Kudu wanda ta kunshi kananan hukumomin Toro, Dass, Tafawa-Balewa, Alkaleri, Kirfi,Bogoro da kuma karamar hukumar Bauchi.

A kwanakin baya ne dai wata kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta yanke hukuncin da ke cewar Lawan Gumau ba shine dan takarar wannan kujerar ba, inda ta yi umurni da cewar Ibrahim Zailani dan karar jam’iyyar a sakamakon zaben fitar da gwani da aka yi na jam’iyyar. Matsalolin dai sun fara samako a asali ne a bisa shigar da kara da Zainani ya yi a gaban kotun yana kalubalantar sakamakon zaben fitar da gwani na jam’iyyar.

Exit mobile version