Kukan Kurciya… Zalama Ba Ta Ba Da Mulki

Daga Abubakar Abba,  Kaduna.

Halin da ake ciki na siyasar kiyayya da rura wutar rikici a sakamakon bambancin kabila da addini a kasar nan babu inda zai kai mu sai rami mai zurfin da idan aka kuskura aka fada fitowa zai yi mugun wuya.

Tun kafin gangar siyasa ta fara zaki a kakar siyasar 2019, ya kamata ‘Yan Nijeriya mu yi wa kanmu kiyamullaili mu dawo cikin hayyacinmu mu fahimci wadanda suke so su kai mu su baro ta hanyar cusa mana kiyayya a kan addini ko kabila. Tarihin da zan biyo da shi na shugabannin da suka gabata zuwa shugabanninmu na yanzu, abin lura ne ga duk maihankali walau a cikin fagen siyasa ko a gefenta.

An binciki Marigayi Cif Obafemi Awolowo akan cin hanci da rashawa karkashin kwamitin bincike na Coker. Daga baya ya fuskanci shari’a a kan cin amanar kasa a gaban wata Kotu. Bai yi zargin cewa an yi ma sa hakan ne, saboda yana Bayarabe ko Kirista ba.

Ya tsaya ya kare kansa da kuma aka hana Lauyan sa Biza, ta shiga Nijeriya, kma dan sa mai ikirarin shi babban Lauya ne a duniya, da ya taho zuwa Kotun don kare shi, ya hadu da hadari a hanya akan hanyar sa ta zuwa Kotun ya mutu, nan Abraham Adesanya ya sanar da Awolawo

labarin lokacin suna zane a Kotun, Abraham ya dauka ko Awolowo zai fara kuka, amma sai bai yi ba, Awolowo ya ankarar da Alkalin Kotun akan abn da ke faruwa,ya kuma nemi izinin ya kare kansa da sauran wadabda ake zaegi.

“Segun ya rasu mu kuma da muke a raye, dole ne a bamu dama mu kare kan mu kada muma mu mutu. Wannan maganar cin amanar ne da farko dole mu kare kan mu wannan tuhuma ce ta cin amanar kasa, kafin mu fara zaman makokin dan mu”

A bisa tarihin, marigayi Awolowo shugaba ne na kwarai da ya jagoranci Alummar sa a bias amana ba kamar sauran shugabanni da ba Alummar su bane a gaban su ba, a kasar nan ba.

Abin da ya kamata ‘yan siyasar mu su son sai sun yi mulki a kota halin kaka ya kamata su duba shine, marigayi Abubakar Tafawa Balewa bai taba faman sai ya zama  Fara  Minista. Shima marigayi Sir Ahmadu Bello ya cancanci ya rike Fara mukamin na Fara Minist a amma ya baiwa Balewa. Tshohon Shugaban kasa Aliyu Shehu Shagari, bai taba tunanin ya zama shugaban kasa ba, amma kuma ya zamo.

Marigayi M.K.O. Abiola ya so ya zama shugaban kasa tun a shekarar 1983, amma bai zama ba har zuwa shekarar 1993. Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo bai yi kamun kafa na ya zama shugaban kasa ba, amma ya zama. Shi kuwa Cif Olu Falae ya so ya zama shugaban kasa tun a shekarar 1992, amma bai zama ba.

Peter Odili ya ya yi iya hakilon sa inda har ya kashe dimbin kudade, amma bai samu ba. Marigayi Umaru Musa Yar’adua bai ma da wata cikakkiyar lafiya, amma ya zamo shugaban kasa ba tare da ya kashe ko kwandalarsa ba. Goodluck Jonathan bai da ko kudin tsayawa takara ko wani kuzarin fafatawa, ammaa ya zamo shugaban kasa.

Tsohon Shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida Mai ritaya da tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abunakar sun nemi su hau kujerar shugaban kasa a 2007, amma tun daga cikin gidan jam’iyyar da suka so tsayawa takara aka kada su.

Muhammadu Buhari bayan ya sha faduwa a takara ya rungumi kaddara, ya kuma sha alwashin ba zai sake tsayawa takara ba. Amma Allah ya zabo shi ya sa ya zama shugaban kasa bayan kusan za a iya cewa ya riga ya fitar da rai a kan kujerar. Lokacin da Buhari ya kara da Jonathan a karon farko, Jonathan bai da wani karfi sosai na fada a ji duk da kasancewarsa shugaban kasa, amma ya kada Buhari, a lokacin da ya kasance ya yi karfi sosai kuma sai gashi Buhari ya kada shi a zaben.

Yemi Osinbajo yana cikin gidansa zaune ya zama mataimakin shugaban kasa daga baya kuma Mukaddashin shugaban kasa. Ku bar duk wani hakilon sai kun yi shugabanci, ku bar komai ga Allah ya yi maku zabi. Ku bar duk kudaden da kuka boye don kashe wa takararku a boye, ku yi amfani da su wajen inganta rayuwar al’ummar ku.

Kukan kurciya jawabi ne, sai dai maihankali yake iya ganewa.

 

Exit mobile version