Connect with us

NAZARI

Kula Da Yara:Abubuwar Da Ke Sa Jarirai Yawan Tusa

Published

on

Yawan tusa ga jarirai abu ne na yau da kullum musamman lokacin da suke a tsakanin sati 3 da haihuwa zuwa watanni 3 zuwa wata 6, saboda hanjinsu bai riga ya yi kwari ba. Haka kuma wasu za su iya wuce wata 6 da haihuwa suna yin tusarsu har zuwa shekara wato watanni 12, sakamakon ba su abin da ake yi da zarar sun kai wata shida musamman rukunin abincin dake gina jiki wato  kamar su irin dafaffen wake a lika musu a abaki, ana ba su kifi, gwaiduwar kifi da dai sauransu, wannan nau’in abincin yana sa su tusa.

Sai kuma inya zamo cewa nonon sa da yake sha zallan sinadarin kurum yafi aka samu babu dan maiko a ciki kamar yadda aka san nono rashin wannan maikon na iya sashi yawan tusa.

Sai kuma in yaro ya zamo mai yawan kuka, wasu yaran har shikewa za ka ji idan suna yin kuka tare da ajiyar zuciya, nan ma a yayin kukan in ana ba su nono koda da akwai maikon to suna iya hadiyar iska shi ma za ta iya sa su tusa domin cikin zai daga alhalin nonon bai isa ba.

Sai bayar da nono akwance shima na sa yaro ya hadiyi iska, cikinsa ya kumbura koda bai yin tusa akai-akai duk sanda ya yi za ta iya yin wari, ballantana inya zamo ana sa masa pampers a kunshe shi.

Wadannan sune abubuwan da ke sa yara kanana yawan tusa.

Tashin Yara Lokacin Bacci

Iyaye da yawa kan yi kuskure yayin tashin kananun yara daga bacci walau jarirai ko kuma wadanda suka fara takawa. Wani lokaci idan ana so su farko ko in za a yi masu wanka sai a tashe su ta yadda bai kamata ba.

Yawanci sai kaga idan jarirai suna bacci kuma ana bukatar a yi masu wanka, sai a dauke su a saka a cikin ruwan dumi, nan za su hau kuka kai saboda sun ji bakon abu. Ko kuma  kaga ana dukan kafafunsu ko a yayyafa musu ruwa domin su farka.   To ku daina hakan domin ba dai-dai bane, ku Sani duk wannan kuskure ne hakan na sa bugun zuciyarsu yana karuwa ba zato ba tsammani. Saboda firgitar da su, wanda hakan ka iya haifar da karancin jini a kwakwalwarsu ko su taso da wata matsalar mai muni tun suna kananu ko kuma hakan ya jawo yaron ya rasa ransa kuma ke kika kasha shi baki sani ba.

Don haka abun da za ku yi, idan za ku tashi yara ko jariri daga bacci ku dawo wajen kansa wato goshinsa a fara hura musu iska a hankali kina kara karfin iskar a hankali za ki ga sun bude ido shi kenan sai su farka.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: