Kunbon Tauraron Dan Adam Na Kasar Sin Zhurong Ya Yi Tafiyar Sama Da Mita 410 A Duniyar Mars

Daga CRI Hausa

Hukumar kula da ayyukan sararin samaniyar kasar Sin CNSA, ta sanar cewar, ya zuwa karfe 20:00 na daren Lahadi agogon Beijing, kunbon tauraron dan adam mai binciken duniyar Mars na kasar Sin samfurin Zhurong ya yi tafiyar sama da mita 410 a kewayen duniya mai launin ja, inda ya kara gudanar da binciken yadda ya kamata.

A cewar CNSA, tauraron dan adam na Tianwen-1 dake kewayawa, ya aje tauraron dan adam na aikin sadarwa, ya yi tafiyar kwanaki 353.

Ayyukan tauraron dan adam na Tianwen-1 na kasar Sin, ya kunshi tafiyarsa, da saukarsa, da kewayarsa, wanda aka harba shi a ranar 23 ga watan Yulin 2020.

Tauraron mai dauke da na’urar binciken ya sauka kasa a shiyyar kudancin duniyar Utopia Planitia, waje mafi girma dake arewacin yankin duniyar Mars, a ranar 15 ga watan Mayu. (Ahmad Fagam)

Exit mobile version