Kungiya Ta Bukaci A Kawo Karshen Yawan Rikice-rikice A Jihar kaduna  

Wata kungiyar tattaunawa domin samar da zaman lafiya a tsakanin addinai (IDFP) ta bukaci shugaban kasan Nijeriya, da Gwamnan jihar Kaduna da dukkan jami’an tsaron kasar nan da su tabbatar sun yi amfani da karfin mulkinsu wajen dakile yawan rikice-rikice da ake yi musamman a jihar Kaduna.

Bishaf Onouha wanda daya ne daga cikin shugabannin kungiyar shine ya yi wannan kiran bayan da kungiyar takai ziyarar gani da ido a jihohin, Zamfara, Kaduna, Binuwai, Taraba da Filato, a wani taro da ta gabatar na bayan ziyarar yau Alhamis a Abuja.

Onouha ya bada misalin dokar hana walwala da gwamnatin Kaduna ta sanya, inda yace ita kadai dokar nan yakamata ta sa mutum ya guji tada fitina, amma dokar ba karamin taimakawa ta yi wajen hana yaduwar rikicin ba, a cewarshi yakamata a yabawa ma gwamnatin jihar bisa wannan kokarin da ta yi.

Bishaf din ya kara da rokon jami’an tsaro da su kara kokari wajen ceto basaraken da masu garkuwa suka sace a jihar Kadunan, Agom Adara Dakta Maiwada Raphael Galadima, har yanzu yana hannun masu garkuwan, kuma jami’an tsaron kadai zasu iya kwato basaraken.

Exit mobile version