Umar A Hunkuyi" />

Kungiya Ta Horar Da Unguwar Zoma 100 A Jihar Nasarawa

Regional Program for Midwife Capacity Building

Wata kungiya mai zaman kanta mai suna, Mother and Child Care Enhancement Foundation (McCEF), ta horas da Unguwar zoma guda 100, a Jihar Nasarawa, a kan kyawawan hanyoyin da ya kamata a bi wajen aikin na Unguwar Zoma a lokacin da suke yin aikin na su.
Kungiyar wacce ba ta gwamnati ce ba, Uwargidan gwamnan Jihar Nasarawa, Hajiya Salamatu Al-Makura, ce ta kirkiro ta.
Horaswan wacce ta dauki kwanaki biyar, an kammala ta ne a ranar Juma’a, a Lafiya, ta kuma sami halartar mata daga kananan hukumomin Lafiya da Obi.
Hajiya Salamatu Al-Makura, wacce ta nuna karancin gudummawar da Unguwar Zoman suke bayarwa a wajen aikin na su na tarban haihuwa, musamman a karkara, ta ce sam bai kamata a raina gudummawar na su ba.
Ta bukaci mahalartan da su yi amfani da abin da suka koya domin inganta aikin na su, wanda zai taimaka masu wajen rage hadurran da ake samu ga uwa da da a lokutan haihuwan.
Ta yi nuni da cewa, a zamanin baya, Unguwar zoma su ne masu taimaka wa mata a wajen haihuwa, wanda hakan ne ya kara nuna bukatar su sami horon da ya dace.
Uwargidan Gwamnan, ta kuma gargadi Unguwar Zoman da su san iyakacin aikin su, domin rage yawan hadurran da ake samu a wajen haihuwan, ba ma a Jihar ta Nasarawa ba kadai a Nijeriya baki-daya.
Uwargidan gwamnan ta bayar da tabbacin cewa, kungiyar na su za ta ci gaba da bayar da duk wani taimakon da ya kamata ga mabukata, ta kuma nemi al’ummar Jihar da su agaza wa mabukata ta yanda su ma za su ji dadi.
Tun da farko, babban shugaban bayar da horon, Mista Adamu Alhassan, cewa ya yi, an cimma nasarar horaswan da aka yi, ya kuma bayyana tabbacin da yake da shi na cewa a halin yanzun Jihar za ta sami sauki a kan yawaitar hadurran da ake samu a wajen haihuwa. A karshen shirin dai an baiwa mahalartan takardun shaida da kuma kayan aiki ga kowace daya daga cikin matan Unguwar zoman.

Exit mobile version