Idris Aliyu Daudawa" />

Kungiya Ta Kaddamar Da Maganin Maleriya Na Musamman

Wata kungiya mai zaman kanta, wadda ba riba take nema ba dangane da su ayyukan da take yi, ta kuma kware wajen maganin zazzabin maleriya ko kuma cizon sauro, ta samu damar kaddamar da wani maganin zazzabin na maleriya, wanda kuma yake daukar zuwa wani takaitaccn lokaci, a kasashen Afirka uku.
Shi dai wannan al’amarin na wayar da kan al’u ana sa ran zai  taimaka ma yara wadanda suka wuce miliyan biyar mma 5.5, wadanda kuma basu kai shekara  biyar ba, a su kasashen uku, saboda su samu kariya daga maleriya, har zuwa lokacin da damina zata wuce.
A wani taron ‘yan jarida wanda suka yi ranar Talata ta wannan makon da muke ciki, kungiyar ta bayyana cewar zata rarraba magunguna wadanda suke maganin maleriya, ga yara wadanda basu kai shekara biyar ba, wadanda kuma suke wuce miliyan biyar a kasashen Burkina Faso, Chadi, da kuma  Nijeriya, nan da watanni hudu masu zuwa.
Shi maganin na zazzabin maleriya ana sa ran zai kare su daga kamuwa da cutar, har tsawon lokacin ruwa.
Kamar dai yadda aka kiyasta kusan rabin al’ummar duniya suna cikin hadarin kamuwa da zazzabin maleriya.
Sai dai kuma kash! Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana cewar kashi 90 na daga  cikin matsalolin da suke da nasaba da maleriya, da kuma kashi 91 na mace -macen da ake yi a sanadiyar ita maleriyar, duk abin ya shafi ita nahiyar Afirka ne.
Hakanan ma kusan kashi 25 na mace – macen da ake yi a duniya a sanadiyar ita cutar abin a kasar Nijeriya ce yake.
Al’amarin ko kuma ayyukan da ita kungiyar take yi abin ya shafii  kasashen 11, wadanda suke cikin Afirka da kuma Kudancin gabashin  Asiya.
Ita dai kungiyar tana taimaka ma al’amuran da suka shafi maleriya ta hanyar rarraba gidajen sauro, wadanda aka sa maganin sauro wanda yake dadewa akan su. Sai kuma aiki da wadanda suke na kulawa da al’amarin daya shafi kula da lafiyar al’umma, saboda a samu bunkasa yadda ake rarraba shi maganin, da kuma sa ido a wasu wuraren da suke da matsaloli na yadda su kwayoyin cutar duk magani da aka saha ya kashe su, abin bai yin wani tasiri akan su.
Hakanan ma sunkawo wanin magani shi zazzabin na maleriya wanda shin a lokaci zuwa lokaci ne, domin ya kasance wani makamin da ake amfani da shi wajen kawo ma al’amarin maleriya tarnaki a nahiyar Afirka. Su dai magungunan sun hada da (amodiakuine plus sulfadodine-pyrimethamine ga dukkanin yara wadanda basu kai shekaru biyar ba lokacin damina.
Shi maganin ana iya shan shi wata- wata wanda kuma ba a son abin ya wuce wata hudu.
Hukumar lafiya ta duniya ta kiyasta cewar akwai yara miliyan 23.7 da suke cikin Afirka,suma sun cancanta a basu SMC, matsayin wani  maganin zai hana ita cutar samun wani tagomashi, a wasu kasashe ko kuma wuraren da suke (Sahel sub-region of Africa). Ko kuma kasashe hudu wadanda yanayin su ya bambanta kwarai, wadannan kasashe sune Burkina Faso, Mali, Nijer da kuma kasar Habasha, basu samun isasshen ruwan sama wannan ma shi yasa akan fuskanci matsalar abinci.
kungiyar mai zaman kanta ta bayyana cewar shi wannan al’amari na yadda za a wayar ma mutane kai akan shi maganin na seasonal malaria, wato wayar da kan al’umma an fara shine a kasashe uku wadanda suke daba bangaren  na Sahel region of Africa.
Ta bayyana cewar shi wannan al’amarin na wayar da kan al’umma, abin ya kunshi ba ko wanne yaro magunguna biyu hadin amodiakuine da kuma sulfadodine-pyrimethamine, sau daya a wata wanda wannan kuma zai dauki tsawon wata hudu yana magani, daga watan Yuli zuwa Oktoba.
“Wannan shine lokacin a cikin shekara wanda ake samun yawan ciwace – ciwace na zazzabin maleriya da kuma mace -mace, a shi sashen na Sahel sub region, kamar dai yadda ya bayyana.”
Su magungunan na maleriya wadanda aka fi sani da SMC wani al’amarin daya shafi jawo hankalin al’umma domin su amince da amfani da shi, a wadancan bangare na kasashen tun shekarar ma  a shekarar 2013.
Darektan  tsarin Christian Rassi ya bayyana cewar shi al’amarin yasa sun kasance cikin farin ciki, tunda dai tsarin na SMC, tuni ya fara yin aiki a kasashen uku.
Ya cigaba da bayanin cewar“Mun yi amfani da makonni wajen horar da wadanda suke rarraba mana magani, da kuma wadanda suke lura da yadda abubuwan suke tafiya, sai kuma maganar tabbatar da cewar magungunan da ake bukata sun isa dukkan wuraren da ake son su kai. Yanzun aikin mu zai far aba tare da bata lokaci ba, saboda dai tuni ne muka dauyri aniyar kare milyoyin kananan yara daga kamuwa da zazzabin maleriya, a wannan lokacin damina kamar dai yadda ya bayyana”.
Ita dai wannan kungiya tana yin aiki ne na kud da kud tsarin yaki da cutar maleriya ta kasa, kai har ma da jihohi da kuma larduna da na kasa da hakan, wato yadda ake kula da lafiyar mutanen karkara, a ko wacce kasa, saboda a samu damar shirya da kuma yadda za atafiyar da tsarin na wayar da kan al’umma.
Shi dai tsarin na wannan shekara an fara yin shine a kasar Burkina Faso ranar 22 ga watan Yuli, sai kuma Chadi da Nijeriyua wanda aka yi ranar 25 ga watan Yuli.
Ita dai wannan manufar ana gabatar da ita ne ta hanyar taimako wanda ya zo daga hadaddiyar daular Turawa ko kuma UK, sai kuma wata Gidauniya ta duniya, da kuma wani tsari na Shugaban kasar Amurka, akan  cutar ta maleriya ko kuma USAID PRESIDENT Malaria Initiatibe, amma kuma wani al’amari daban wadanda suka fi bayar da gudunmawa,mutane ne wadanda su aikin su ke nan da kuma taimako na mutane daban – daban.
Cutar maleriya dai tana cigaba da kasancewa  babbar matsalar data shafi al’amarin lafiyar al’umma, musamman  a kasashe 97, wadanda suke cikin kasashen, da rana ke fitowa sau daya  a cikin shekara, wannan kuma yana faruwa a lokacin bazara ko kuma rani. Wani kuma sashe ne na duniya wanda yafi ko ina zafi, da kuma akwai yanayi biyu da suka hada da Rani da kuma Damina. Wannan bangare kuma ya kunshi yawacin nahiyar Afirka, Kudancin Asiya, Indonesiya, Sabuwar Guinea, Arewacin kasar Australiya, da dai sauran wasu kasashen. Shi kuma Subtropics an fi yin zafi ga kuma matsalar guguwa wadda take yi barna matuka, wanda ake kira da suna Hurricane ko kuma Typhoon. kasashen kuma sune New Delhi, Hong Kong, Anthens, Cairo da kuma Medico city.
A duniya gaba daya akwai matsalolin da suka shafi ita cutar maleriya kusan miliyan 214, a ko wacce shekara sai kuma mutane fiye da biliyan  3.3 daga kasashe 106 na duniya, na da yiyuwar kamuwa da ita cutar. Sai kuma yawan mace -mace da suka kai ku san 438,000 wadanda kuma an danganta su ne da cutar ta maleriya, musamman ma Afirka ta Kudu da kuma Sahara, inda ma aka kiyasata cewa an samu mutuwar  mutane kashi  90  cikin dari, a sanadiyar cutar maleriya.

Exit mobile version