Connect with us

LABARAI

Kungiya Ta Tallafa Wajen Canza Rayuwar ‘Yan Sara Suka 300 A Bauchi

Published

on

Wata kungiya mai zaman kanta mai suna, ‘Center for Jubenil Delinkuency Awareness in Nigeria’, ta shirya wa matasa ‘yan sara-suka su dari uku 300 shiri na musamman domin gyara musu halinsu don su kasance jakadu na kwarai a kowani lokaci.

Shugaban kungiyar ta CJDAN, Hajiya Halima Baba Ahmad ita ce ta shaida hakan jimkadan bayan kammala wani horaswa da suka shirya wa matasan a Bauchi domin gyara musu halinsu kan shaye-shaye, da sauran muggan dabi’un da suke jifa kawukansu a ciki.

Halima Baba Ahmad ta kara cewa matasa da dama suna tsunduma kansu cikin harkar sara-suka, tada hankulan jama’a, sata, gami da shaye-shayen miyagun kwayoyi wanda ya fi kamari a tsakanin matasan ba tare da tunanin illolin da hakan zai yi wa rayuwarsu na gaba ba.

Ta ce, “muna sauyawa da kuma gyara halin matasa fiye da sekaru. Ya zuwa yanzu, daruruwan matasa ne muka samu nasarar sauya musu halinsu daga gurbacewa zuwa turba na gari ta hanyar zaunar da su a aji mu horar da su illoli da kuma shirin yadda za su samu zarafin kyautata rayuwarsu. Mafi yawan matasan da muke basu kulawar sun kasance cikin sara-suka wadanda a wasu lokutan sukan iya kashe mutum, wadannan aiyukan sun kasance marasa kyau, mun yi kokarin sauya musu halinsu har muka daurasu suka gane cewar dabi’ar bata da kyau wanda hakan zai kaisu ga zama jakadu na kwarai,” Inji ta

Halima tana mai shaida cewar wasu matasan daga cikin wadanda suka samu gyara halinka daga kungiyar suna cikin dardar kan halin da suka kasance a baya, amma ta shaida cewar, “Ina mai tabbatar muku yanzu dukkanin matasan da muka horar gabaki daya sun sauya halinsu daga mummunar dabi’ar da suke yi. Sun kuma rumgumi hanya madaidaiciya wacce za ta kaisu ga gina kasa da ci gaban zaman takewa, kana za su kasance jakadun zaman lafiya a cikin al’ummominsu,” A cewar Halima

Ta kuma kara da cewa, “wasu da dama daga cikinsu sun samu horo kan sana’o’i daban-daban, mun kuma maida wasu zuwa makarantu. Ko a wannan karon ma, mun riskar da wasu zuwa makarantun addini, mun kuma horar da wasu yadda za su samu nasarar cin jarabawar kammala sakandari, wasu kuma sun samu nasarar kammala karatun diploma, mun assasa yadda za su samu zarafin taimaka wa kasar nan,” A cewar Shugaban kungiyar ta CJDAN.

Wasu da dama daga cikin wadanda suka yi jawabi a wajen taron, sun shawarci matasan da su yi duk mai iyuwa domin kauce wa sake komawa cikin dabi’arsu ta jiya wanda a cewarsu hakan ba zai taimaki rayuwar tasu da komai ba, kana sun shawarci matasan su kasance masu gudanar da kyawawan dabi’u a cikin al’umma domin samar da jama’a masu cikakken tarbiyya.

Da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida, Mai Unguwar Gwallaga, Mallam Dandada Ahmadu ya shaida cewar muddin matasan suka himmatu da ababen da aka daurasu a kai ba za su sake samun kansu a cikin masu tayar da hankulan jama’a ba.

Ahmadu ya nemi iyaye da gwamnati da suke dauran rayuwar gyara tarbiyar matasa da muhimmanci domin gina kasa mai cikakken ci gaba da wanzuwar zaman lafiya.

Ya kuma shawarci matasa masu samun horon da su kasance masu kyautata rayuwarsu a kowani lokaci domin ci gaban kasa da wanzuwar tattalin arziki.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: