Wata kungiya mai zaman kanta mai suna ‘Zainab Tessy Friends of Fistula Foundation’ a makon jiya ne ta kaddamar da gangamin wayar da kan iyaye mata da ‘yan mata matakai da kuma hanyoyin kariya daga kamuwa da cutar Yoyon Fitsari da ke tagayyara matan da suka kamu da shi a kananan hukumomin Kirfi da Alkaleri da ke jihar Bauchi.
Taron wayar da kan mata da ‘yan matan wanda ya samu halartar dandazon mata daga kananan hukumomin biyu, hakan ya faru ne a sakamakon rahotonnin yawaitar masu kamu da cutar da ake samu daga yankunan.
Wasu mata biyu da suka yi jinyar cutar masu suna Hajara Bello da Malama Rakiya Ali daga kauyen Lumi da ke Kirfi, sun bayyana cewar lokacin da suka kamu da cutar sun fuskaci tsangwama da kyama daga wurin jama’a musamman mazajensu, inda suka tabbatar da cewa dogon nakuda ne ya jawo musu hakan da kuma tauna hakwara a lokacin da suke kokaron haihuwa.
Sai dai dukkaninsu sun shaida cewar an yi musu tiyata wajen ciro ‘ya’yan da ke cikinsu, kana an yi musu jinyar cutar kyauta a asibitin gwamnati da ke Ningi. Dangane da matakin kiyaye kai daga hakan kuwa, sun ce sun dauri tsarin bada tazarar haihuwa domin kiyayesu daga yawaitar tiyata da ake musu duk lokacin da za su haihu.
Ya ce, “Huji ake samu tsakanin yadda matan ke haihuwa da mafitsara da kuma wajen bayan gida, duk inda aka samu huji a nan za a iya samun cutar.
“Abun da yake jawo yoyon fitsari yawanci rashin kula ne. Mace ya kamata idan tana da juna biyu ta zo awu a asibiti lokacin ne za a gane watanni nawa ne cikin, ya kan yaron yake da sauran matakan lafiya dai. Lokacin da za ta haihu ma ta je asibiti ta haihu a can, idan awanni haihuwa ya wuce kwararrun likita za su duba su ga abun da ya dace; da zarar aka wuce awa takwas mace ta na nakuda to akwai matsala, kwararru za su duba dan ne ya yi girma ko kuma kugun ce ta yi karama, nan take za a turata babban asibiti domin mata tiyata ba tare da wani matsala ba.
“Amma idan mace ba ta zo awu ko zuwa haihuwa a asibiti ba, ba za a gane wannan matsalar ba, zai zama tana da shan wahala kila matsala ne wanda kwararru ne kawai ke iya ganowa, in an samu irin hakan sai ka ga mace ta samu matsalar yoyon fitsari,” a cewar shi.
Dakta Dada ya ce babu gaskiya a batun cewa aure da wuri na kawo matsalar yoyon fitsari, “Ko an yi wa yarinya aure da wuri muddin za ta je awu za a san yadda za a shawo kan matsalarta in ma akwai, za kuma ta haihu abunta lafiya. Ba wai karar mace ke kamu da cutar ba, za ka iya samun uwa ‘yar shekara arba’in ko ma fiye ta kamu da cutar, muddin dai za a je awu to lallai za a samu mafita daga cutar,” a fadin shi.
Da take bayyana wa ‘yan jarida dalilinta na kafa wannan Gidauniyar, Shugabar Gidauniyar, Misis Zainab Tessy Haly ta ce, a bisa nazarin wahalhalun da matan da suka kamu da cutar ke sha, ta ga ya dace ta himmatu wajen nusar da matan bin matakan da suka dace domin ganin ba su kamu da cutar ba balle ma a je ga jinya.
“Manufarmu bai wuce wayar da kai da ilmantar da al’umma musamman ‘yan uwana mata dangane da batun cutar Yoyon Fitsari. Da farko su fahimci menene yoyon fitsari kuma ta yaya ake kamuwa da shi da me za a yi don kariya daga kamuwa da shi din.
“Abun da ya jawo hankalina ga daukar wannan aikin shine, Allah ya bani dama kula da jinyar masu irin wannan cutar na yoyon fitsari, muna zama da su a kowani lokaci na kuma san menene damuwarsu. Na zauna na yi nazari a matsayina na mace, na ce da irin wannan wahalar da su ke sha da kyamatarsu da ake yi, ya dace in ga na tashi tsaye wajen bada gudunmawata ta hanyar kiyaye kamuwa da wannan damuna na yoyon fitsarin, wannan shine dalilin,” Inji ta.
“Don haka matanmu da suke fama da wannan cutar su daina zama da shi a gida su fita su je asibitin nan domin a yi musu jinya.
“Kuma wani abun da wasu jama’a ba su sani ba, musamman na karkara shi jinyar wannan cutar kyauta ne komai da komai da za a miki a asibiti kyauta ne don haka a daina kyamatar masu dauke da cutar a daure a kaisu asibiti,” inji Madam Tessy.
Ta jawo hankalin mazaje da su daina kyamatar matayensu a lokacin da suka kamu da cutar, ta kuma bayyana cewar tana gudanar da kungiyar ne da dan abun da take samu na daga albashinta, amma ta neman kungiyoyi su tashi tsaye wajen taimaka wa mata a wannan fannin.
A cewar Madam Tessy, “Hanyoyin kiyaye kamu da cutar yoyon fitsari sun hada da; inganta tsarin kula da juna biyu, tabbatar da nakuda da haihuhuwa a asibiti a maimakon gida, cin abinci masu gina jiki ga yara mata masu juna biyu, amfani da robar fitsari ga mata masu nakuda, musamman ga masu dogon nakuda,” a fadinta.