Isa Abdullahi Gidan Bakko" />

Kungiyar Al’ummar Rano A Zariya Ta Tallafa Wa Juna Ce  –Dan Iya Rano

Exif_JPEG_420

Mun kafa kungiyar ci gaban al’ummar karamar hukumar Rano da ke jihar Kano, mazauna Zariya a, domin tallafa wa junanmu ta bangarori da dama da kuma kula da duk wasu abubuwa da suke gudana a mahaifarmu karamar
hukumar Rano ta jihar Kano’’ Babban ma’ajin kungiyar ci gaban al’ummar Rano da suke zaune a Zariya Dan‘iya Sani Rano ya bayyana kalaman da suka gabata, a lokacin da wakilinmu da ke Zariya ya zanta da shi, inda ya amsa tambayoyin wakilinmu kan dalilin kafa wannan kungiyar da kuma ayyukan da kungiyar ke aiwatarwa shekara fiye da goma sha biyu da suka gabata.
Alhaji Dan’iya ya ci gaba da cewar, kadan daga cikin ayyukan wannan kungiya sun hada da tallafa wa duk wani dan kungiya day a tsinci kan sa a wasu matsaloli, musamman a bangaren kasuwanci dad a rashin lafiya
da dai sauran matsaloli ma su yawan gaske, da dan adam ke tsintar kan sa daga lokaci zuwa lokaci.
Ma’ajin kungiyar al’ummar Rano da suke Zariya ya kara da cewarAlhaji Dan’iya ya ci gaba da cewar, kungiyarsu na da tsare – tsare da suke aiwatarwa domin tallafa wa mambobinta da suka shafi in dan kungiya na gudanar da harkar kasuwanci, sai ya sami matsala, ya  ce kungiya kan shiga gaba, na ganin an warware wa mamban da ya shiga matsalar, ba tare da wanda ya shiga matsalar ya biya wani abu daga aljihunsa ba.
Game da duk wani dan kungiya da ba shi da lafiya,, ko kuma iyalansa, in har kungiya ta lura ya na bukatar taimako, shugabannin kungiya na yanke hukumcin rungumar matsalar mamban da hannu biyu, kuma a warware ma sa a kan lokaci, wannan, kamar yadda ya ce, sun yi wa mambobin kungiya da dama.
Sauran ayyukan da wannan kungiya ke aiwatarwa domin tallafa wa mambobin kungiyar , a cewar babban ma’ajin kungiyar sun hada da tallafa wa marayun da mambobin kungiyar suka rasu,y ace sun aiwatar da shi da dama. Wani abin koyi da ya kamata sauran kungiyoyi su yi koyi da wannan kungiyar, a cewar Alhaji Dan’iya, shi  ne yadda kungiyar ke tallafa wa duk wani dan asalin karamar hukumar Rano0, ko da bai yi rijsta da kungiyar.
Domin kara hada kan al’ummar Rano da suke karamar hukumar Zariya da a duk inda suke, a sassan Nijeriya kuma, Alhaji Dan’iya ya shawarce su da suka hada da kungiyar al’ummar Rano da suka samu, domin ci gabansu da kuma karamar hukumar Rano baki daya.
A dai zantawarsa da wakilinmu Alhaji Dan’iya  ya yaba wa mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris, na yadda ya rungumi al’ummar Rano da suke Zariya tun daga lokacin da mai martaba Sarkin Rano ya gabatar da su a gareshi, ‘’ ya mayar da mu tamkar ‘yan asalin masarautar Zazzau’’, in ji shi.
Da kuma ya juya ga ‘yan asalin karamar hukumar Rano da suke Zariya, sai ya yi kira garesu da su ci gaba dab a shugabannin duk goyon bayan da suka kamata da kyawawan shawarwarin da zai zama ma su silar ciyar da kungiyar da ‘ya’yan kungiyar gaba  da kuma karamar hukumar Rano da jihar Kano baki daya.
A karshe, Alhaji Dan’iya ya jinijna wa Alhaji Usman Nadada, tsohon jami’in ‘yan sanda da ya taba zama a Zariya, dan asalin karamar hukumar Rano, na yadda ya rungumi wannan kungiya da hannu biyu tare dab a kungiyar duk wani tallafi da ta bukata, a nan sai ya yi kira ga sauran ma’aikata da kuma ‘yan kasuwa ‘yan asalin karamar hukumar Rano,
da su rika koyi da Alhaji Nadada, wajen tallafa wa al’ummar Rano da suke gida da sauran sassan Nijeriya.

Exit mobile version