Kungiyar ANGO Ta Yi Tir Da Karkatar Da Kayayyakin ’Yan Gudun Hijira

Daga El-Mansur Abubakar, Gombe

Wata kungiya mai zaman kanta da ba ta gwamnati ba a Gombe mai suna ANGO ta yi Allahwadai kan yadda a kwanakin bayan a ka karkatar da kayayyakin jin kai, wanda kwamitin farfado da shiyyar arewa maso gabas da shugaban kasa ya kafa ya aiko na miliyoyin Naira, don taimakawa ’yan gudun hijirar.

Wannan batu ya na dauke ne a wata takarda mai dauke da sa-hannun shugaban kungiyar, Ibrahim Yusuf, da ya aike wa manema labarai a Gombe.

Ya ce, wani bincike da su ka gudanar ya tabbatar mu su da son zuciya da kuma rashin adalcin da babban sakataren hukumar ta SEMA, Dakta Danlami Arabs Rukuje, da wani jami’nsa su ka nuna.

Takardar ta kuma nuna cewa, a kwanakin nan a ka gano wata babbar mota dauke da kayayyakin gini na miliyoyin Naira da a ka turo jihar, don raba wa ’yan gudun hijira, wanda PCNI ta samar a wasu shagunan mutane da wuraren ajiya, wanda jami’an hukumar EFCC su ka kama a fadar jihar Gombe, inda suka tabbatar da an karkatar da kayayyakin ne, don biyan bukatar babban sakataren hukumar ta SEMA, wanda tuni su ka damke shi su ke ci gaba da gudanar da bincike a kan sa.

Ya ce, kungiyar ta yi tsaye wajen bai wa hukumar ta EFCC hadin kai da goyon baya wajen cigaba da yaki da ta ke yi da cin hanci.

Ibrahim Yusuf, a takardar ya nuna cewa, su na nan sun jajirce wajen yin amfani da kudadensu da al’umma da duk wata hanya da ta dace, don yin amfani da ita wajen bai wa EFCC hadin kan da zai sa ta cigaba da yaki da rashawa.

Wakilinmu ya sami labarfin cewa, wannan kungiya ta ANGO uwa ce kungiyoyi 80, wadanda ba na gwamnati ba (NGOs) masu rijista da su ke da ofis a kananan hukumomi 11 na jihar ta Gombe.

Exit mobile version