Connect with us

LABARAI

Kungiyar CAN Ta Goyi Bayan Sake Takarar Shugaba Buhari

Published

on

Shugabani na kasa na kungiyar “Change Adbocates of Nigeria” CAN a takaice da kuma kungiyar ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje sun amince da sake neman wa’adi na biyu da shugaba Muhammadu Buhari ke nema na shugabancin kasar nan a shekarar 2019.

A sanarwar da kungiyar ta fitar wadda shugaban matasa na kungiyar, Gabriel Nwajei, ya sanya wa hannu, aka kuma raba wa mane ma labarai a garin Asaba, sun kuma nuna amuncewarsu da takarar tshohon gwamnan jihar Edo Adams Oshiomhole, na kujerar shugabancin jam’iyyar APC a taron jam’iyyar na kasa da za a gudanar a wannan shekarar 2018.

Sanarwar ta ce, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna jajircewa wajen daukan mataki a kan shawarwarin da suka shafi rayuwar ‘yan Nijeriya yadda ya kamata, a saboda haka ne suke kira gare shi daya sake kara wa’adi na biyu saboda ya samu kammala aiyukan alhairin daya farad a ‘yan Nijeriya, suna masu cewa, a halin yanzu babu wani gurbi a fadar Aso a shekarar 2019. “Shirinsa na yaki da cin hanci da rashawa da kuma karbo kudaden sata daga ciki da wajen kasar nana bin a yaba ne.

“ya kuma fitar da kasar nan daga rikicin tattalin arzik, ya kuma kara bunkasa aikin noma a cikin kasa, in da aka samu karin noma shinkafa da rogo da sauran kayayakin gona, ga kuma shirin nan na N-Power wanda matasa ke amfana da shi.

“shugaba Buhari ya kuma sa hannu a kan dokan nan na ‘Not too Young to Run” ya kuma samar wa majalisun jihohi da bangaren shari’a na jihohi cin gashin kansu.

“Ya kuma bayar da lambar yabo ga marigayyi M.K.O.Abiola da Ambasada Babagana Kingibe da kuma Chif Gani Fawehinmi dac kuma mayar da ranar 12 ga watan Yuni ta zama ranar dimikradiyya”

Kungiyar ta kuma amince da cewa, har yanzu a kwai sauran aikin daya kamata ayi don samun cikakken bunkasar kasar nan a fannin samar da tsaro da sake fasalin kananan hukumomi da kuma hanyoyin gudanar da zabe cikin adalci ba tare da magudi ba.

“Amma sanin kowa ne ba dare daya ake cimma gaggarumin buri irin wannan ba”

“Burinmu shi ne fadakar da jama’a don su karbi katin kuri’arsu saboda a samu gaggarumin nasara a zaben shugaban kasa na shekarar 2019’.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: