Bello Hamza" />

Kungiyar CAN Ta Yi Tir Da Kashe Fasto 2 A Abuja Da Kaduna

A ranar Laraba ce kungiyar Kiristoci ta CAN ta mika ta’aziyyarta ga kungiyar ‘Roman Catholic Church’ dana ‘Nigerian Baptist Conbention’ a bisa mutuwar Fastoci biyu

Sanarwa ta fito ne daga shugaban kungiayr, Reb Samson Ayokunle a takardar da fasto Adebayo Oladeji, shugaban sashin watsa labarai na kungiyar ya sanya wa hannu a Abuja, ya yi Allah wadai da kashe kashen gaba daya.

Ayokunle ya ce, malaman addinin kiristan sun gamu da ajalinsunne a yayin da wasu ‘yan bindiga da aba asan ko su wanene ba suka harbe su a garin Abuja da Kaduna.

Ya kara da cewa, a harbe marigayyi Reb. Michael Akawu,a garin Gwagwalada ne a yayin day aje kasuwa yin siyayya ranar 18 ga watan Agusta.

Washe gari ne kuma wasu da ake zargin cewa, Fukani makiyaya ne suka kai hari cocin ‘Nasara Baptist Church’ dake Guguwa kusa da Rigasa a garin ta jihar Kaduna.

“wadanda ake zargin nan take suka harbe Reb. Hosea Akuchi suka kuma yi aw gaba da matarsa mai syna Talatu Akuchi.

“har zuwa yanzu ba a san inda take ba, wadanda suka kumayi garkuwa da ita sun bukaci sai an basu naira Miliyan 5 kafin su saketa,” inji shi.

Daga nan ya nuna bakin cikinsa a kan tsananin rashin tsaro a fadin kasar nan, ya kuyma bukaci gwamnatin arayya ta kara kaimi don tabbatar da tsaro da zaman lafiya a kasar nan.

Ya kuma kara da cewa, a halin yanzu babu inda ake da aminci a fadin kasar nan, ‘yan ta’adda da ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane suna harkokinsu babu kakkautawa, ya kuma kara da cewa daga dukkan alamu jami’an tsaro sun shagala da harkar zabe dake tafe, jagororin a kasa kuma sun mance wadanda ake kashe wa ne suka zabe zuwa karagar mulkin da suke tunkaho dashi.

Exit mobile version