Connect with us

LABARAI

Kungiyar CONEV Ta Yaba Wa Gwamnan Bauchi Kan Habbaka Ilimi

Published

on

Wata kungiyar farar hula ta masu kada kuri’u mai suna, ‘Congress of Nigerian Eligible Voters’ (CONEV) a takaice, ta jinjina wa gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar dangane da muhimman aiyukan da ya samu nasarar gudanarwa a jihar musamman kan sha’anin ilimi.

Kungiyar ta yi wannan yabon ne a cikin makon jiya a sa’ilin da suka gudanar da wani jerin gwanon nuna wa gwamnan jihar goyon bayansu kan yadda yake tafiyar da mulkin jihar ta Bauchi, suna masu shaida cewar M.A din ya taka rawa sosai ta fuskokin ci gaban jihar da tala kanjihar.

Da yake jawabinsa a mashigar gidan gwamnatin jihar Bauchi, shugaban kungiyar na kasa, Kwamared John Ngene Offia ya shaida cewar shirye-shiryen gwamnan kan ilimi musamman na gyara makarantu, daukan karin malamai, kyautata sha’anin ciyarwar daliban makarantun firamare, samar da motocin sintiri kan duba yayin ilimi a jihar, gyarawa hadi da samar da dakunan kwanan malamai, sun yi gayar habakar da sashin ilimi da daukaka darajar ilimi a jihar ta Bauchi, wanda shugaban ya bayyana cewar gwamnan ya cancanci gayar yabo kan wannan fannin.

Ya ke cewa, shirin gwamnatin mai ci kan bayar da ilimi kyauta na gayar taimaka wa dubban iyaye a jihar da kuma saukakar da hanyar kyautata ilimi a jihar ta Bauchi, inda yake bayanin cewar dalibai da iyayensu da dama ne suka ke cin gajiyar shirin gwamnan kan sha’anin ilimi kawo yanzu.

Shugaban, John Ngene Offia ya daura da cewa a bisa muhimman aiyukan ci gaba da gwamnan ya iya samar wa jama’an jihar, a matsayinsu na wannan kungiyar za su tashi tsaye wajen samar wa gwamnan dubban masu jefa kuri’u domin ya samu nasarar ci gaba da kyautata jihar da tala kanjihar.

Ya ce, “Za mu tabbatar a zaben 2019 mun samar wa gwamnan tulin kuri’u domin ya samu zarafin ci gaba da kyautata shugabanci a jihar Bauchi,” inji Kungiyar

Da yake maida jawabinsa, gwamnan jihar Bauchi wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar Bauchi, Alhaji Muhammad Nadada Umar ya gode wa kungiyar a bisa duba gayar aiyukan alkairi da gwamnatin take yi hadi da yaba mata.

Gwamnan yana mai shan alwashin cewar ya zuwa yanzu sun himmatu wajen kyautata rayuwar jama’an jihar ta Bauchi.

Daga bisani gwamnan ya yi alkawari wa matasan jihar, inda ya shaida cewar nan da mako daya ko biyu mataimakin shugaban kasar Nijeriya zai kasance a jihar Bauchi domin kaddamar da asibitin koyar da sana’a ga matasa, ya shaida cewar an shirya wannan ne domin samar wa matasan jihar aiyukan yi da kuma shirinsu na dakile zaman kashe wando a tsakanin al’umma.

Kungiyar dai ta jagoranci zanga-zangar nuna goyon baya wa gwamnan jihar, inda suka zaga cikin jihar hadi da kitse hancin zagayen nasu a gidan gwamnati wanda suka samu gayar tarba daga sakataren gwamnatin jihar ta Bauchi.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: